Shekara 5 kenan ko waya bai taba yi min ba - Mahaifin Mikel Obi ya fakewa dan sa laya

Shekara 5 kenan ko waya bai taba yi min ba - Mahaifin Mikel Obi ya fakewa dan sa laya

Bayan sace shi da masu garkuwa da mutane suka yi kwanakin baya, mahaifin fitaccen dan wasan kwallon kafa, John Mikel Obi, ya bayyana irin alakar dake tsakaninsa da dan nasa.

An sace mahaifin Mikel Obi, dattijo mai shekaru 74, a Makurdi ta jihar Benuwe yayin da yake kan hanyar sa ta zuwa Enugu domin halartar wani taro na 'yan uwansa.

Wannnan shine karo na biyu da masu garkuwa suka taba sace mahaifin na Mikel Obi tun bayan sace shi a karo na farko a shekarar 2011.

Shekara 5 kenan ko waya bai taba yi min ba - Mahaifin Mikel Obi ya fakewa dan sa laya
John Mikel Obi da mahaifinsa

Da yake ganawa da manema labarai, Mikel Obi, ya tabbatar da cewar ya samu rahoton sace mahaifin nasa sa'o'i 4 kafin buga wasan Najeriya da kasar Argentina a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya, amma duk da haka ya danne damuwar sa tare da buga wasan.

Saidai mahaifin Obi ya bayyana cewar dangantaka tsakanin da dan nasa ta dade da lalacewa kuma duk kokarin gyara ta ya ci tura.

DUBA WANNAN: Jarumin Fim ya ci al-washin lashe zaben gwamnan jihar sa a APC

"Dangantaka tsakanina da shi ta dade da lalacewa. Ban yi masa wani laifi ba, amma mun fi shekaru 5 ko waya bamu yi ba. Amma yana kiran mahaifiyar sa.

"Nayi iyakar kokarina domin gyara dangantakar mu amma haka ta bata cimma ruwa ba. Bana jin ciwon hakan domin ubangiji ya fada min kada na damu kuma muddin ina ganinsa a akwatun talabijin yana taka leda, to babu damuwa," a cewar mahaifin Mikel Obi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel