Wata sabuwa: Mahaifi na na nan da ran sa - Inji dan Mu'ammar Gaddafi

Wata sabuwa: Mahaifi na na nan da ran sa - Inji dan Mu'ammar Gaddafi

Babban da ga marigayi shugaban kasar Libiya Mu'ammar Gaddafi watau Saiful Islam a wata fira da manema labarai ya yi karin haske game da mutuwar mahaifin sa kimanin shekaru da dama da suka gabata.

Majiyar mu dai da dama daga kasar Ivory Coast ta ruwaito cewa Saiful Islam ya ce wata mata mai suna Zayraf Aya dake a kauyen su Marigayi Gaddafin ta bayyana cewa tsohon shugaban kasar yana da rai kuma tana ganin sa akai-akai kuma yanzu haka yana jinya amma da zaran ya samu lafiya zai koma kasarsa don ceto al'umarsa.

Wata sabuwa: Mahaifi na na nan da ran sa - Inji dan Mu'ammar Gaddafi
Wata sabuwa: Mahaifi na na nan da ran sa - Inji dan Mu'ammar Gaddafi

KU KARANTA: Buhari ya yaudari talakan Najeriya - Turaki

Legit.ng ta samu cewa Haka ma dai matar mai shekaru 35 a duniya ta yi ikirarin cewa Mu'ammar Gaddafi din shine mahaifin 'yar ta kuma tace ya rasa kafar sa daya sakamakon hare-haren bama-baman da aka kai masa, a lokacin aka nemi hambarar da mulkinsa.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa biyo bayan wata guguwar sauyi da ta tashi a yankin gabas ta tsakaiya an ruwaito cewa yan tawayen kasar Libiya sun hambarar da gwamnatin Mu'ammar Gaddafi a shekarar 2011.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel