Mata 'Yan siyasa sun fi gaskiya da rikon amana - Obasanjo

Mata 'Yan siyasa sun fi gaskiya da rikon amana - Obasanjo

A ranar Juma'ar da ta gabata ne tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo, ya nemi Mata a kasar nan kan su kara kaimi tare da bayar da himma wajen cudanya cikin harkokin siyasa.

Obasanjo ya bayyana cewa, daga cikin kwarewa da kuma fahimtar sa a harkokin siyasa, ya lura cewa Mata sun yiwa Maza fintinkau tare da wankin babban bargo ta fuskar aminci na jajircewa kan rikon gaskiya da amana.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin halartar taron gudunmuwa da tallafawa Mata wajen damawa cikin harkokin gwamnati, siyasa da wuraren aiki wanda wata Cibiyar harkokin watsa labarai fasaha da al'adu ta Najeriya ta gudanara a babban birni na Ibadan dake jihar Oyo.

Mata 'Yan siyasa sun fi gaskiya da rikon amana - Obasanjo
Mata 'Yan siyasa sun fi gaskiya da rikon amana - Obasanjo

Dattijon arzikin ya hikaito dalilai dangane da yadda yawaitar Maza 'yan siyasa da ake gurfanar wa bisa laifukan rashawa da cin amanar gwamnati idan an kwatanta da na Mata da wasu dalilai daban-daban a matsayin shaida ta furucin sa.

A yayin gabatar da jawaban sa Obasanjo ya bayyana cewa, gudunmuwar da Mata ke bayar wa ga kowace kasa tana habaka tattalin arziki. "Babu wata kasa da za ta kasance mai girma muddin rabin al'ummarta sun ƙare ne kawai a ɗakunan dafa, ko kuma nuna wari da bambanci wajen kulawa da Mata."

KARANTA KUMA: Zambar Haraji: Ronaldo ya biya Fan 12.1m ga Kasar Spain

A sanadiyar haka ne tsohon shugaban ya yi kira kan kawar da shamakin da ake yiwa Mata domin samun damar taka matakai da matsayi na girma cikin harkokin siyasa musamman ta hanyar tursasa ilimi kuma kyauta ga 'ya'ya Mata.

Ya kara da cewa, ya kamata a haramta auren mata a kananun shekaru, tare da dagewa wajen tursasa su samun ilimi tun daga matakin firamare har zuwa manyan makarantu na gaba da sakandire.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel