Takaitaccen tarihin Tsohon Sufetan ‘Yan Sandan Najeriya da ya rasu

Takaitaccen tarihin Tsohon Sufetan ‘Yan Sandan Najeriya da ya rasu

A yanzu za ku san ko wanene Marigayi tsohon Sufeta Janar na ‘Yan Sandan Najeriya Ibrahim Commassie wanda ya rasu jiya Alhamis. Ibrahim Coomassie shi ne Shugaban Kungiyar nan ta Dattawan Arewa watau ACF.

1. An haifi Ibrahim Coomassie a shekarar 1942 kuma yana cikin ‘Ya ‘yan Amadu Coomassie wani tsohon ‘Dan Bokon Arewa kuma manyan Ma’aikatan Gwamnatin Yankin.

2. Coomassie yayi karatu ne a Makarantar nan ta Barewa, daga nan ya zarce zuwa wasu Makarantu na aikin ‘Yan Sanda a Kasashen waje na Amurka da kuma Birtaniya.

KU KARANTA: Allahu Akbar: Wani Tsohon IGP na Najeriya ya rasu

3. Bayan Coomassie ya san aiki ya rika ne aka nada sa Shugaban ‘Yan Sandan Kasar nan a 1993. Coomassie ya bar mukamin sa ne ranar da Olusegun Obasanjo ya hau mulki a 1999.

4. A lokacin Ibrahim Coomassie yana IG na ‘Yan Sanda ne aka kama MKO Abiola ba tare da bin ka’ida ba. MKO Abiola din dai ya mutu ne a cikin gidan Yari daga baya.

5. A 1996 ne Shugaban ‘Yan Sanda ya kama binciken wasu barna da ‘Yan Sandan Najeriya su kayi a lokacin Janar Babangida inda aka rika wasu kashe-kashe wanda ya zargi Turawa.

6. Bayan rasuwar Janar Sani Abacha a 1998 ne Coomassie da Tawagar sa su kai yi Iyalin Marigayin Ta’aziyya inda aka Matar Abacha ta nemi ya kama wanda ya kashe Abacha.

7. Gwamnatin Obasanjo ta kama Ibrahim Coomassie a shekarar 1999 lokacin da ta ke bincike game da kisan Marigayiya Kudirat Abiola da kuma Janar Shehu Musa ‘Yaradua.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel