Buhari ya bukaci tabbatar da Ingawa a matsayin shugaban FCSC

Buhari ya bukaci tabbatar da Ingawa a matsayin shugaban FCSC

A ranar Alhamis, 19 ga watan Yuli majalisar dattawa ta tabbatar da samun wasikar Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya bukaci a tabbatar da Dr. Bello Ingawa daga jihar Katsina a matsayin shugaban hukumar daukar ma’aikata na tarayya.

Buhari ya kuma tura da sunayen mutane 12 kan a nada su a matsayin kwamishinoni.

Sunayen wadanda aka tura sune: Waziri Ngurno, Borno; Bello Mahmoud – Jigawa; Ahmed Sarna, Kebbi; Iyabode Odulate-Yusuf, Ogun; Shehu Danyaya, Niger; Fatai Adebayo, Oyo; Ejoh Chukwuemeka, Anambra; Joe Poroma, Rivers; Ibrahim Mohammed, Kaduna; Aminu Sheidu, Kogi; Simon Etim, Akwa Ibom.

Buhari ya bukaci tabbatar da Ingawa a matsayin shugaban FCSC
Buhari ya bukaci tabbatar da Ingawa a matsayin shugaban FCSC

Sai dai kuma bukatar tabbatar da Ingawa da wasu mutane 12 a matsayin kwamshinoni ya tada kura inda wasu yan majalisa suka yi zargin cewa akwai son kai a lamarin.

KU KARANTA KUMA: Rade-radin sauya sheka: Gwamna Ortom ya isa hedkwatar APC domin ganawa mai muhimmanci tare da shugabannin jam’iyyar

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu, ya tada jijiyar wuya akan cewa akwai bangaranci wajen nada shugabannin hukumomin gwamnati.

A cewarsa, nade-naden baya-bayan nan da shugaba Buhari yayi da kuma wadda yake neman amincewar majalisa ya nuna cewa wadanda aka zaba duk yan yankin kasar guda ne.

Shugaban masu rinjaye, Ahmad Lawan, ya yi jayayya kan cewa nade-naden yayi daidai “idan akayi duba ta fuskanci masu yawa.”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel