Ruwa ba ya tsami banza: Masoyan Tinubu sun fara zargin Buhari da niyyar kassara maigidansu bayan zaben 2019

Ruwa ba ya tsami banza: Masoyan Tinubu sun fara zargin Buhari da niyyar kassara maigidansu bayan zaben 2019

Wasu ‘yan siyasa dake biyayya ga Bola Ahmed Tinubu daga yankin kudu maso yamma na ‘yan kabilar Yoruba sun fara nuna shakku a kan goyon bayan shugaba Buhari a zaben 2019.

A yayin da zaben shekarar 2019 ke kara matsowa, magoya bayan Tinubu sun shiga tararrabin makomar maigidansu bayan kamala zabukan shekarar ta 2019.

‘Yan siyasa, masoya Tinubu, da suka rike mukamai dabab-daban a gwamnatinsa lokacin da yake gwamnan jihar Legas, na cigaba da nuna kokwanto a kan shawarar Tinubu ta sake mara wa shugaba Buhari baya ya zama shugaban kasar Najeriya a karo na biyu.

Ruwa ba ya tsami banza: Masoyan Tinubu sun fara zargin Buhari da niyyar kassara maigidansu bayan zaben 2019
Tinubu da Buhari

Masoyan na Tinubu da suka nemi a boye sunansu, sun shaidawa jaridar ThisDay cewar mai yiwuwa Buhari na son yin amfani da Tinubu ne domin samun kuri’ar jihar Legas da ma ta yankin kudu maso yamma a zaben 2019 sannan ya juya masa baya.

Daya daga cikin masoya Tinubu day a kasance daya daga cikin ‘yan majalisar zartarwar gwamnatin jihar Legas daga shekarar 2003 zuwa 2007 ya tabbatar da cewar sun matsawa Tinubu lamba a kan ya sake duba shawarar goyon bayan Buhari a zaben 2019 domin shugaba Buhari bai wani ja shi a jiki ba duk da irin gudunmawar day a bayar a shekarar 2015.

DUBA WANNAN: Tura ta kai bango: Al’umma a jihar Kano sun yi barazanar kauracewa zaben 2019

Ya kara da cewar, “hankalin Buhari bai kwanta da irin karfin da Tinubu ke da shi ba a yankin kudu maso yamma da ma fadin Najeriya ba a saboda zai iya kokarin kassara shi bayan zaben 2019.”

Tuni dai jita-jita tayi nisa kan cewar wasu gwamnonin yankin kudu maso yamma sun fara hada kai domin yakar karfin da Tinubu ke da shi a zaben gwamnan jihar Osun mai zuwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel