Maduro: Afirka ce ta lashe wasan kwallon kafa na duniya da aka buga a Rasha

Maduro: Afirka ce ta lashe wasan kwallon kafa na duniya da aka buga a Rasha

Shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro ya ce, Nahiyar Afirka ce ta samu nasarar lashe gasar cin kofin duniya na kwallon kafa, wanda aka buga a kasar Rasha

Maduro: Afirka ce ta lashe wasan kwallon kafa na duniya da aka buga a Rasha
Maduro: Afirka ce ta lashe wasan kwallon kafa na duniya da aka buga a Rasha

Shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro ya ce, Nahiyar Afirka ce ta samu nasarar lashe gasar cin kofin duniya na kwallon kafa, wanda aka buga a kasar Rasha.

Shugaban kasar yayi jawabin ne a wurin wani taro da aka gudanar a kasar ta Venezuela inda yake cewa, "Kungiyar kwallon kasa ta kasar Faransa ce ta lashe kofin duniya, amma kungiyar kamar ta 'yan Afirka ce, tun da asali 'yan Afirka sunfi yawa a 'yan wasan, kuma hakan ya samo asali ne a lokacin da iyayen 'yan wasan suka yi gudun hijira zuwa kasar ta Faransa daga Afirka."

DUBA WANNAN: Labarin wata 'yar Afirka data bar muhimmin tarihi a duniya

Yace, yana fatan dai kasashen Turai zasu daina nunawa bakaken fata banbanci da wariyar fata, musamman ma 'yan Afirka, sannan kuma yana fatan zasu daina kyamar 'yan gudun hijira.

Shugaba Maduron ya cigaba da cewa, "Suna yiwa nahiyar Afirka kallon wuri mai wahala, bayan sun sace arzikin nahiyar, kuma sai gashi 'yan Afirka ne su ciyowa kasar Faransa kofin duniya.

A karshe Maduro ya taya shugaban kasar Rasha Vladimir Putin murnar nasarar da kasar sa ta samu wurin karbar bakuncin gasar cikin kwanciyar hankali da nasara.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel