A watan gobe zaku ji nawa ne karin albashi zai kai - inji kungiyar kwadago

A watan gobe zaku ji nawa ne karin albashi zai kai - inji kungiyar kwadago

- Albashi a Najeriya yai na ko'ina a duniya kankanta

- A watan Agusta zuwa Satumba ne za'a ji bayanai kan nawa aka daidaita

- Tun 2010 rabon da a kara wani albashi a Najeriya

A watan gobe zaku ji nawa ne karin albashi zai kai - inji kungiyar kwadago
A watan gobe zaku ji nawa ne karin albashi zai kai - inji kungiyar kwadago

Albashin Ma'aikata, na tarayya, wanda karancinsa bai fi N18,000 cikin shekaru 10, zai sami dan tagomashi bayan da aka tsayar da yarjejeniya kan ko nawa ne za'a qara, tsakanin kungiyoyin kwadago da gwamnatin tarayya.

Sakataren kungiyar ta TUC, yace a saurara, zuwa watan Agusta, za'a ji daga bakin ministan ayyuka, Dakta Chris Ngige, wanda a baya yayi alkawarin zai farantawa ma'aikata rai.

DUBA WANNAN: Tsokacin Sheikh Dahiru Bauchi kan kashe-kashe

Su dai kungiyoyin kwadago, sunce kamata yayi mafi karancin albashin ya kai N54,000 ga kowanne ma'aikaci, kwatankwacin dala 160 kenan a kowanne wata, wanda duk da haka shima yayi kadan, amma gwamnati na kukan cewa batta da kudi.

A 2015 da 2016 ne aka sami tashin gwauron zabin daloli, inda sai da ya kai har N500 ga dala daya, a kuma lokacin ne, kudaden kasar nan na kasar waje suka yi kasa bayan uwar sata da aka tafka a zamunnan mulkin PDP da ma na soji ba a baya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel