Sheikh Dahiru Bauchi yayi tsokaci kan wadannan kashe-kashe da suka qaru a kasar nan

Sheikh Dahiru Bauchi yayi tsokaci kan wadannan kashe-kashe da suka qaru a kasar nan

- Kashe-kashen da ake kamar sun kai inda ba'ayi tsammani ba

- Ance Fulani ne makiyaya ne ke kashe-kashe kan shanunsu da ake sacewa

- Malam Dahiru Bauchi yayi tsokaci

Sheikh Dahiru Bauchi yayi tsokaci kan wadannan kashe-kashe da suka qaru a kasar nan
Sheikh Dahiru Bauchi yayi tsokaci kan wadannan kashe-kashe da suka qaru a kasar nan

Sanannen malami, Shehi Dahiru Usman Bauchi yace ba fulani bane ke kashe kashe a wasu sassa na kasar nan ba, ya kara da cewa kashe kashen bashi da dangantaka da addinai.

Shehi Bauchi ya fadi hakan ne a amsa tambayoyin yan jaridu da yayi a ranar laraba biyo bayan hargitsin fulani da makiyaya da kuma wasu bangarori na kasar nan.

Yace: "Fulani ba baki bane a Najeriya, kowa yasan su a matsayin yare da ake mutuntawa. Idan da makasa ne, da sun fara nuna halinsu a shekaru daruruwa da suka gabata ba wai sai yanzu ba. Kawai makasan na boyewa ne da rigar fulanin don su bata wa yaren suna. An san fulani da sanduna, kwari da baka amma wadannan da ake magana, bindigogi garesu. Waye ya ba fulani bindiga? Wannan aikin gwamnati na da ta tsamo masu laifin, tare da hukunta su."

Malamin yace: "Idan mutum yayi ta'addanci, kamata yayi a gano shi sannan ya fuskanci hukunci. Fulani suna zama da kowa lafiya a duniya, akan wanne dalili zasu dau makamai don yakar mutanen da suke tare dasu?"

DUBA WANNAN: Kasashen da suka dauki kofin duniya tunda aka fara gasar

Kamar yanda yace, yana daga cikin hakkin gwamnati, kare rayuka da dukiyoyi, hana zubar da jini, kare iyalai da kuma martabar mutane.

"Su kuma hakkin yan kasa shine sauraron hukuma, bada hadin kai don samun zaman lafiya mai dorewa."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel