Ga kida ga dukiya: Attajiran Mawakan da ake da su a Najeriya

Ga kida ga dukiya: Attajiran Mawakan da ake da su a Najeriya

Wannan karo mun leka Duniyar kudi ne inda mu ka kawo maku jerin Mawakan da su ka fi kowa kudi a cikin Mawakan da ake ji da su a kaf Najeriya. A jerin za ku ji cewa akwai irin P-Square da Wizkid da Davido.

Ga kida ga dukiya: Attajiran Mawakan da ake da su a Najeriya
2 Face Idibia wanda yayi wakar African Queen yana cikin Attajiran Mawaka

1. P-Square

A jerin da aka fitar kwanakin baya, babu wanda ya sha gaban P-Square wajen dukiya a Najeriya. Tagwayen ‘Yan wasan sun ba sama da Naira Biliyan 15 baya a yanzu.

2. Don Jazzy

Wanda ya zo na 2 a jerin kamar yadda mu ka samu labari daga Forbes shi ne Don Jazzy mai sama da Biliyan 6. Don Jazzy ya kan shirya waka ne kuma shi ne Mai gidan irin su Korede Bello, Iyanya, Tiwa Sawage.

3. DBanj

D Bank wanda aka fi sani da “The Koko Master” ya tada abin da ya zarce Naira Biliyan 5 a kasar nan. Babban Mawakin ya kan samu kudi ne har ta hanyar tallace-tallace a Duniya.

KU KARANTA: Mai kamfanin Amazon Jeff Bezos ya ba Dala Biliyan 150 baya

4. 2 Face

Wanda yake na 4 a jerin shi ne 2 Face Idibia wanda yanzu abin da ya tara gaba da baya ya zarce Biliyan 4.5. A bara ma dai fitaccen Mawakin da ya dade yana bugawa yayi tashe kwarai.

5. Davido

Na 5 a jerin dai si ne Adedeji Adeleke David wanda akafi sani da Davido. Matashin Mawakin wanda yanzu yake tashe ya mallaki Naira Biliyan 2.9, kuma har a kasar waje ana ji da shi.

6. Wiz Kid

Wanda yake bin Davido a baya shi ne Wiz Kid wanda shi ma Matashin Mawaki ne. Wiz Kid ya tada kai da Biliyan Naira Biliyan 2.8. A bara dai Mawakin yayi zarra a Duniya baki daya.

7. Flavor

Chinedu Okoli yana cikin Attajiran Mawakan da ke Najeriya. Flavor kamar yadda aka fi sanin sa, ya mallaki fiye da Naira Biliyan 2.5. Flavor ya sha gaban irin su Banky W, Iyanya Timaya da sauran su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel