Gwamnatin Tarayya za ta tallafa tare da biyan diyya ga wadanda Ambaliyar ruwa ta afkawa a jihar Katsina - Osinbajo

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa tare da biyan diyya ga wadanda Ambaliyar ruwa ta afkawa a jihar Katsina - Osinbajo

A ranar Talatar da ta gabata ne gwamnatin tarayya ta daura damara tare da kudirta aniyyar tallafawa wadanda ibtila'in ambaiyar ruwa ta afkawa a karamar hukumar Jibia dake jihar Katsina.

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, shine ya kudirta wannan furuci yayin da ya ziyarci yankin da ibtila'in ya afku domin jajintawa wadanda lamarin ya shafa a jihar ta Katsina.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya bayyana, Osinbajo ya wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen gudanar da wannan ziyara inda ya jajantawa gwamnatin jihar Katsina da kuma wadanda annobar ta shafa.

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa tare da biyan diyya ga wadanda Ambaliyar ruwa ta afkawa a jihar Katsina - Osinbajo
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa tare da biyan diyya ga wadanda Ambaliyar ruwa ta afkawa a jihar Katsina - Osinbajo

Mataimakin shugaban kasar ya bayar da tabbacin gwamnatin tarayya na tadanar kayan tallafi da kuma agaji ga wadanda ibtila'in ya afkawa, inda ya ce gwamnatin za ta dauki muhimman matamakai domin kiyaye afkuwar wannan annoba a lokuta na gaba.

Legit.ng ta fahimci cewa, tawagar mataimakin shugaban kasar ta hadar har da shugban cibiyar bayar da agaji na gaggawa domin tabbatar da kudirin na fadar shugaban kasa.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya ƙi amincewa da wasu dokoki 4 na Majalisar Tarayya

Osinbajo ya kara da cewa, gwamnatin tarayya za ta hada hannu da gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna Aminu Bello Masari domin biyan diyya da kuma tallafawa wadanda annobar ta shafa.

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan annoba ta afku ne a karshen makon da ya gabata da tayi sanadiyar salwantar rayukan sama da mutane 50 da kuma rushewar gidaje da a halin yanzu mutane sama da 1000 sun rasa mahallan su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel