Matakai 10 da shugaba Buhari ya dauka dangane da Kashe-Kashe a kasar nan - Fadar Shugaban Kasa

Matakai 10 da shugaba Buhari ya dauka dangane da Kashe-Kashe a kasar nan - Fadar Shugaban Kasa

A ranar Litinin din da ta gabata ne fadar shugaban kasa ta mayar da martani tare da kare martaba kan tuhumar shugaban kasa Muhammadu Buhari, dangane da suka da caccakar sa kan kashe-kashe dake faman afkuwa a fadin kasar nan.

Shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomhole tare da kungiyar kare hakkin musulmi ta MURIC, sun bayyana cewa shugaba Buhari na iyaka bakin kokarin sa dangane da kawo karshen ta'addancin kashe-kashe sabanin yadda wasu al'umma da kafofin watsa labarai dake tuhumar sa da yiwa lamarin rikon sakainar kashi.

Kungiyar ta MURIC ta shawarci al'ummar kasar nan kan kauracewa zargin shugaba Buhari da laifin nuna halin ko oho kan kashe-kashe, inda ta ce musabbabin sa bai wuci kabilanci, yaduwar jita-jita da shaci fadi gami da majalisar tarayya dake kara ta'azzara lamarin a kasar nan.

Matakai 10 da shugaba Buhari ya dauka dangane da Kashe-Kashe a kasar nan - Fadar Shugaban Kasa
Matakai 10 da shugaba Buhari ya dauka dangane da Kashe-Kashe a kasar nan - Fadar Shugaban Kasa

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya bayyana, Legit.ng ta kawo muku jerin matakai 10 da gwamnatin shugaba Buhari ta dauka dangane da kashe-kashe kamar yadda kakakin sa, Mista Femi Adesina ya bayyana.

1. Hukumar 'yan sanda ta kasa ta baza jami'an ta na musamman masu leken asiri a jihar Benuwe bayan mummunan ta'addancin da ya afku a da ake zargin makiyaya ke da alhakin aiwatar da shi tun a watan Janairun 2018.

2. Majalisar zantarwa ta kafa kwamitin mutum 10 wanda mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ke jagoranta domin aiwatar da binciken diddigi kan rikicin makiyaya da manoma a kasar nan.

3. Hukumar Sojin kasa reshen jihar Kaduna ta dabbaka wani sabon shiri na musamman mai taken Operation Karamin Goro tare da hadin gwiwar hukumar sojin kasa, 'yan sanda, DSS da Civil Defence domin magance ta'addancin garkuwa, fashi da makami, da kuma satar shanu a yankunan jihar Kaduna da Neja.

4. Hukumar Sojin kasa ta kaddamar da gudanarwar Operation Ayem Akpatuma a jihohin Benuwe, Taraba, Kogi, Nasarawa, Kaduna da kuma Neja domin tunkarar ta'addancin garkuwa da mutane da kuma rikicin makiyaya da manoma.

5. Hukumar Sojin sama ta tanadi wasu jiragen sama na zamani masu da kansu domin zirga-zirga da yawon leken asiri gami da dauko rahotanni na tsaigumi dare da rana a yankunan Arewa maso Gabas.

DUBA WANNAN: Buhari da Osinbajo sun halarci Jana'izar Mahaifiyar Fasto Bakare a Birnin Abeokuta

6. Hukumar Sojin sama ta kafa sabbin shiyoyi da rassa cikin yankunan wasu jihohi da dama a kasar nan domin magance matsaloli da annoba musamman ta rikicin makiyaya da manoma.

7. A watan Mayun da ya gabata kuma hukumar tsaro ta kasa ta tanadi dakaru 1000 tare da baza su wanda ta tsakuro daga sojin sama, sojin kasa, sojin ruwa, 'yan sanda da kuma DS domin tunkarar barazanar tsaro a yankunan Arewa maso Kudu da Arewa ta Tsakiya.

8.A watan Mayun dai, Sufeto Janar na 'yan sanda Ibrahim K. Idris, ya baza jami'an sa 200 da motocin kai komo da zirga-zirga a babbar hanyar Birnin Gwari dake tsakanin jihar Kaduna da Zamfara domin fatattakar ta'addanci.

9. Shugaban hafsin sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Yusuf Tukur Burataim ya tanadi sabbin motoc 49 na yaki ga dakaru dake reshen barikin Azare a jihar Bauchi domin magance matsalolin tsaro a Arewacin jihar Borno.

10. Hukumar Sojin sama ta kuma tanadi jiragen sama masu saukar ungulu ga reshen ta dake Gusau domin tallafawa yakokin ta kan ta'addanci a jihar Zamfara da kewaye.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel