Siyasar Kano: Kwamishinan Ganduje ya dauki alwashin tika Kwankwaso da kasa

Siyasar Kano: Kwamishinan Ganduje ya dauki alwashin tika Kwankwaso da kasa

A yayin da babban zaben shekarar 2019 ke cigaba da karatowa, su kuwa yan siyasa na cigaba da aune aunen hanyar da za ta kasance mafita a garesu, musamman dangane da abinda ya shafi bukatar tsayawa takarkaru da lashe zabe.

A nan ma dai, Kwamishinan albarkatun noma na jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna ne ya bayyana kwadayinsa a fili, ta hanyar bayyana bukatarsa ta tsayawa takarar kujerar Sanatan Kano na tsakiya, kujerar da Sanata Rabiu Musa Kwankwao ke walawa akanta a yanzu haka.

KU KARANTA: Cin amana ruwa ruwa: Yadda Maigadi ya tafka ma Maigidansa mummunar ta’asa

Siyasar Kano: Kwamishinan Ganduje ya dauki alwashin tika Kwankwaso da kasa

Siyasar Kano

A yayin da yake bayyana bukatar tasa, Gawuna ya yabi kansa a matsayin dan siyasa daya tilo a jihar Kano, da baya tsoron fuskanta tare da yin kara kaina da duk wani abokin hamayya, duk girmansa a siyasance, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito.

Gawuna ya kara da cewa tsaf zai iya kada Kwankwaso a takarar kujerar Sanatan Kano ta tsakiya, duk da cewa Kwankwaso ne ke rike da kujerar a yanzu, kuma tsohon gwamna ne, tsohon Minista, tsohon mataimakin Kaakakin majalisa, tsohon jakada, haka zalika tsohon Maigidan gwamna Abdullahi Ganduje.

Sai dai ba komai bane ya janyo har su Gawuna ke shinshinar kujerar Kwankwaso ba, illa rikicin iko da ya barke a tsakanin Kwankwaso da Gwamna Abdullahi Ganduje, jim kadan da ya mika ma Gandujen ragamar mulki.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar NAIJ.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna El-Rufai ya samu sarauta a Kaduna

Girma ya karu: An yiwa El-Rufa'i sarauta

Girma ya karu: An yiwa El-Rufa'i sarauta
NAIJ.com
Mailfire view pixel