Tabbas ina nan a kan bakata ta sayan Arsenal - Dangote

Tabbas ina nan a kan bakata ta sayan Arsenal - Dangote

Attajirin dan kasuwa da yafi kowane bakar fata kudi a Afrika ,Alhaji Aliko Dangote ya jadada cewa har yanzu yana kan bakarsa na son sayar kungiyar kwallon kafa ta Arsenal dake Ingila.

Dangote yace da zarar ya kammala aikin matatan man fetur da yake ginawa a kan kudi $10 biliyan, zai mayar da hankalinsa kan batun sayan kungiyar ta Arsenal.

Idan an kammala matatan man, zata rika samar da gangan mai 650,000 a kowace rana kuma hakan ya nuna cewa zata zama matatan mai mafi girma a nahiyar Afirka.

Tabbas ina nan a kan bakata ta sayan Arsenal - Dangote
Tabbas ina nan a kan bakata ta sayan Arsenal - Dangote

Dangote ya yi wannan maganar ne yayin wata hira da ya yi da Financial Times da aka wallafa a ranar Laraba 11 ga watan Yulin shekarar 2018.

DUBA WANNAN: Har ila yau: Wata gobarar dare ta kone shaguna kurmus a kasuwar garin Kano

A kididigan adadin arzikin da attajiran duniya suka mallaka da Bloomberg ta wallafa cewa Damgote ya mallaki $12.4 biliyan, wannan na nuna ya dara wanda yafi kowa hannun jari a kungiyar Arsenal, Stan Kroenke, da $4.4 biliyan.

"Idan na sayi kungiyar, zan inganta ta yadda masu goyon bayan kungiyar ke bukatar suka ta kasance"

Wannan dai ba shine karo na farko da Dangote ya nuna sha'awar sayar kungiyar ta Arsenal ba.

A watan Satumban 2016, ya shaidawa gidan talabijin na Bloomberg cewa "Babu makawa" zai saya Arsenal "matsalar ba ta kudi bane"

"Wata kila cikin shekaru uku zuwa hudu," inji shi.

"Matsalar shine akwai wasu ababen da suka shige min gaba. Da zarar na kawar dasu, zan mayar da hankali kan batun cinikin."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel