Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai tafi kasar Holland gobe

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai tafi kasar Holland gobe

Bayan dawowarsa daga kasar Mauritania, Shugaba Muhammadu Buhari zai tafi kasar Netherland a nahiyar Turai domin halartan taron murnan zagayowar ranan amincewa da amfani da dokar Roma a matsayin kundin babban kotun duniya ICC.

Legit.ng ta samu wannan labari ne a wani jawabi da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya saki a yau Asabar.

Garba Shehu ya bayyana cewa : "Shugaba Buhari zai tafi ne gobe Lahadi, 15 ga watan Yuli 2018 inda zai gabatar da jawabi a babban kotun. A cewar Garba Shehu, Buhari kadai ne shugaban kasa a duniya da zai gabatar da jawabi a taron.

Bayan taron, shugaba Buhari zai tattauna da babban lauyan kotun, Ms Fatou Bensouda. Kana zai gana da alkalin alkalan kotun, Chile Eboe-Osuji, wanda asalinsa dan Najeriya ne.

Bugu da kari, shugaba Buhai zai gana Firam Ministan Holland, Mart Ruttr, domin tattaunawan diflomasiyya kuma zasu rattaba hannu kan wasu yarjejeniya."

KU KARANTA: Ana can yanzu haka ana kulla ta tsakanin manyan PDP da Obasanjo

Wadanda za su raka shugaba Buhari sune gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong; gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu; karamar mininstan masana'antu, Aisha Abubakar; ministan harkokin wajen Najeriya, Geofrey Onyeama; da ministan Shari'a, Abubakar Malami.

Sauran Sune minisatan noma, Audu Ogbeh; Shugaban kamfanin NNPC, MaikantiBaru; shugaban ma'akatar tashar jirgin ruwa, Hadiza Bala Usman.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel