Yadda wani dan shekaru 17 ya tsira daga gidan matsafa a Kano

Yadda wani dan shekaru 17 ya tsira daga gidan matsafa a Kano

Wani matashi mai shekaru 17 dake karatu a Bauchi, Salihu Yahaya, ya bayar da labarin yadda ya sha da kyar bayan masu yankan kai sun kama shi a Kano.

A hirar da ya yi da kamfanin dillanci labarai na kasa (NAN) a Bauchi, dalibi yace makonni uku bayan kubutarsa daga gidan yankan kan, har yanzu bai gama dawowa hayyacinsa ba.

Kamar yadda ya fadi, bayan an kama su, an kai su wani gida da ba zai ya ganewa ba a yanzu kuma an sanya musu tufafi masu launin ja shi da wasu yara guda 18 kuma da isarsu aka yanku guda 16 daga cikinsu.

Yadda wani dan shekaru 17 ya tsira daga gidan matsafa a Kano
Yadda wani dan shekaru 17 ya tsira daga gidan matsafa a Kano

DUBA WANNAN: Abin tausayi: Wasu tagwaye da aka dauka aikin 'dan sanda tare sun mutu rana guda

"Ina zaune a gaban gidanmu a misalinm karfe 12 na ranar 23 ga watan Yuni sai wasu mutane biyu suka tsaya a mota suna tambaya ta wata gidan biredi dake kusa da gidanmu.

"Dama gidan biredin zan tafi sai na amince in shiga motar tare dasu don in kai su.

"Da shiga ta cikin motan sai na rasa inda nake kuma lokacin da na farka sai na tsince ni a wani gida sanye da jajayen tufafi masu lamba tare da wasu yaran 18 kuma duk anyi mana aski," inji shi.

Daga nan ne fa aka fara yanka wasu daga cikin mu a gaban mu.

"Muna kallo yadda wani mutum ya taho tare da wasu kati, suka daure hanayen yaron na farko kuma suka yanka shi sannan suka tare jininsa cikin wata roba.

"Lambar riga ta itace ta 18 amma lokacin da aka yanka na 16, sai mutumin yace ya gaji kuma ya bayar da umurnin a mayar da mu a kulle a daki sai zuwa safiyar ranar 23 ga watan Tuni zai cigaba da mu.

Yahaya yace bayan an mayar dasu dakin misalin karfe 3 na dare sai masu gadin suka ce kansu na ciwo saboda haka zasu tafi siyo 'Panadol' bayan tafiyarsu ne muka lura cewa kofar a bude take kuma muka bude sai muka gano cewa gidan da muke bata da katanga kuma muna cikin dokar daji ne.

"Dagan nan ne muka fara gudu cikin dokar daji har sai da na fadi sumamen, a lokacin da na farka sai na tsinci kaina a ofishin yan sanda a Kano."

Yahaya yace har yanzu bai fara zuwa makaranta ba saboda firgita da ya yi sakamakon abinda ya gani a gidan yankan kan.

Mahaifin yaron, Yahaya Yerima, ya tabbatar da afkuwar lamarin sai dai bai yi hira da NAN ba saboda yana ta shirye-shiryen bikin diyarsa da zai aurar a ranar 14 ga watan Yuli.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel