Gwamnonin APC 5 sun hadu da Tambuwal a Sokoto

Gwamnonin APC 5 sun hadu da Tambuwal a Sokoto

Gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) biyar a jiya sun gana da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na kimanin sa’o’i uku a gidan gwamnatin jihar Sokoto.

Hasashe na karuma na cewa Tambuwal na shirye-shiryen komawa jam’iyyar PDP wanda ya barin a yayin zaben 2015 lokacin yana a matsayin kakakin majalisar wakilai.

Kafin ganawar, Gwamna Abdulaziz Yari, wadda ya jagoranci auran gwamnonin, ya bayyana cewa sun je jihar ne domin yiwa Tambuwal da mutanen Sokoto da kuma iyalan wadanda aka kashe a harin karamar hukumar Rabah ta’aziya.

Gwamnonin APC 5 sun hadu da Tambuwal a Sokoto
Gwamnonin APC 5 sun hadu da Tambuwal a Sokoto

Sauran gwamnonin da suka yi ganawar sun hada da na Borno, Kashim Shettima; Adamawa, Jibrilla Bindow; Jigawa, Badaru Abubakar; Katsina, Aminu Masari; da kuma na Niger, Abubakar Sani Bello.

KU KARANTA KUMA: Wani Sanata ya nemi a tsige Gwamnan Zamfara Yari daga ofis

Sannan, jim kadan bayan ta’aziyan, gwamnonin sun shiga ganawar sirri.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel