Zubar da jini: Wannan ba shine Buharin da talakawa suka zaba ba a 2015 - Tambuwal

Zubar da jini: Wannan ba shine Buharin da talakawa suka zaba ba a 2015 - Tambuwal

Gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Aminu Tambuwal ya yi tsokaci tare da tambihi mai daukar hankali a game da kashe-kashen da ke aukuwa a kusan dukkan sassan kasar nan inda ya bayyana cewa ba abun da talakawan kasar suka zaba ba kenan a shekarar 2015.

Gwamnan dai ya bayyana hakan ne a lokacin da yake nuna alhinin sa akan mutane sama da 30 da wasu 'yan bindiga suka kashe a kauyen karamar hukumar Rabbah ta jihar Sokoto.

Zubar da jini: Wannan ba shine Buharin da talakawa suka zaba ba a 2015 - Tambuwal
Zubar da jini: Wannan ba shine Buharin da talakawa suka zaba ba a 2015 - Tambuwal

KU KARANTA: Rahama Sadau ta kayatar a cikin sabbin hotunan ta

Legit.ng ta samu cewa gwamnan dai ya nuna matukar rashin jin dadin sa game da kisan sannan kuma yayi wa iyalan mamatan ta'aziyya tare da addu'ar samun zaman lafiya a jihar da ma kasar baki daya.

A wani labarin kuma, Majalisar wakilan Najeriya a ranar Laraba ta bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau Independent National Electoral Commission, INEC da ta sake duba yiwuwar canza ranakun zabukan fitar da gwani na jam'iyyun kasar.

Wannan kiran dai kamar yadda Honorable Balarabe Salame daga jihar Sokoto ya gabatar da kudurin, ya ce ya zama dole ne musamman idan akayi la'akari da yadda ranakun suka zo kwana biyu kacal kafin ranar Arfa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel