Kashe-kashe: Ku kara hakuri hukumomin tsaro na suna aiki tukuru – in ji Buhari

Kashe-kashe: Ku kara hakuri hukumomin tsaro na suna aiki tukuru – in ji Buhari

- Shugaba Bhari ya nemi da ayiwa shugabannin hukumomin tsaron uziri

- Wannan na biyo bayan bukatar tsige su da mutane suke kira da ayi

- Amma sai dai shugaban da alama ba zai yi hakan ba

A jiya Laraba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci yan kasar nan akan su kara hakuri akan irin kashe-kashen da ake y a wasu sassan kasar nan, domin gwamnatinsa tana matukar bakin kokarinta

Kashe-kashe: Ku kara hakuri hukumomin tsaro na suna aiki tukuru – in ji Buhari
Kashe-kashe: Ku kara hakuri hukumomin tsaro na suna aiki tukuru – in ji Buhari

Ya kuma bayyana cewa jami'an rundunar tsaro ta kasa suna bakin kokarinsu wajen tabbatar da samun wanzajjen zaman Lafiya.

KU KARANTA: Tukur Buratai na lanca wasu manyan ayyuka a shalkwatar tsaro dake Abuja

Wannann jawabin yana cikin wata sanarwa da babban mai taimakawa shugaban kasa akan harkokin yada labarai Mal. Garba Shehu ya sanyawa hannu.

Sanarwar ta Kara da cewa shugaban kasa Muhammad Buhari ya yi Allah wadai da irin adadin mutanen da aka kashe ciki har da wani Hakimi, a kauyen Gandi da ke karamar hukumar Raba a jihar Sokoto.

Haka zalika sanarwar ta gargadi duk masu yunkurin tada zaune tsaye da su kuka da kansu domin duk wanda aka kama zai dandani kudarsa.

Sakamakon barkewar rikice-rikice daban-daban ne a sassan kasar nan mutane suka rika kiraye-kirayen a sauya su domin sun gaza.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel