Rikicin APC ya canja salo: Buba Galadima na R-APC ya aike da wasikar neman soke zaben su Oshiomhole ga INEC

Rikicin APC ya canja salo: Buba Galadima na R-APC ya aike da wasikar neman soke zaben su Oshiomhole ga INEC

Rikin jam’iyyar APC ya dauki sabon salo bayan shugaban tsagin R-APC, Buba Galadima, ya aike da wasikar neman rushe zaben shugabannin APC ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).

A cikin wasikar ta sa, Galadima, ya shaidawa INEC cewar zaben shugabannin jam’iyyar APC na ranar 23 ga watan Yuni day a samar da Adams Oshiomhole a matsayin shugaba, cike yake da saba ka’ida da taka dokokin jam’iyyar APC da na hukumar zabe.

Domin kafa hujja a kan ikirarinsa na saba doka yayin zaben shugabanninn jam’iyyar ta APC, Galadima, ya aike da wani faifan bidiyo dake nuna yadda aka sabawa doka yayin gudanar da zabukan shugabannin.

Rikicin APC ya canja salo: Buba Galadina na R-APC ya aike da wasikar neman sike zaben su Oshiomhole ga INEC
Rikicin APC ya canja salo: Buba Galadina na R-APC ya aike da wasikar neman sike zaben su Oshiomhole ga INEC

“Na rubuta wannan takarda ne a matsayina na daya daga cikin mutanen da suka kafa APC kuma daya daga cikin ‘yan kwamitinta na amintattu dake da kada kuri’a a zabukan jam’iyyar domin jawo hankalin INEC a kan yaudarar da aka shirya da sunan zaben sabbin shugabanni a ranar 23 ga watan Yuni da kuma zaben da aka gudanar ranakun 2, 5 da 8 ga watan Mayu na shugabannin mazabu, kananan hukumomi da jihohi.

DUBA WANNAN: Tsiyar Nasarar: Sanata, dan majalisar wakilai da bulaliyar majalisa a jihar Fayose sun koma APC

“Wadannan zabuka cike suke da saba doka da karya ka’idojin zabe kamar yadda yake a sashe na 20(1) na kundin tsarin mulkin APC,” a cewar Galadima.

Zamu kawo maku Karin bayani da zarar hukumar INEC ta bayyana matsayinta a kan takardar da Galadima ya aike mata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel