Abinda ka shuka: Wasu ‘yan tamore sun hallaka wani magidanci day a kasha surukar sa a jihar Kebbi

Abinda ka shuka: Wasu ‘yan tamore sun hallaka wani magidanci day a kasha surukar sa a jihar Kebbi

A yau, Talata ne, wasu matsa ‘yan tamore suka hallaka wani magidanci, Tambaya Manu, mai shekaru 42 bisa zarginsa da kashe surukar sa a jihar kebbi.

Lamarin ya faru ne a kauyen Bangu na garin Mahuta dake karamar hukumar Fakai a jihar ta Kebbi.

Wani shaidar gani da ido, da bai yarda a ambaci sunansa ba, ya shaidawa jaridar The Nation cewar Manu ya kasha surukar sa ne saboda sun hana shi ganawa da matarsa, Aisha, da ya yiwa saki daya.

Ya saki matarsa ne bayan wani sabani ya shiga tsakaninsu kimanin watanni 4 da suka wuce. Bayan mutuwar aurensu ne sai ta koma gidan mahaifinta, da yanzu bay a raye.

Abinda ka shuka: Wasu ‘yan tamore sun hallaka wani magidanci day a kasha surukar sa a jihar Kebbi
Gwamnan jihar Kebbi; Atiku Bagudu
Asali: Depositphotos

“Duk kokarin yin sulhu domin ganin Aisha ta koma gidan Manu ya ci tura, hakan ya saka Manu zuwa gidan su Aisha dauke da sharbebiyar wuka da ya yi amfani da ita ya yanka sururkar ta sa domin mayar da matar sa gidansa,” a cewar shaidar.

Shaidar ya kara da cewa, “Manu ya yi yunkurin kasha wasu mutane biyu a gidan su Aisha amma makwabtan da suka taru bayan sun ji hayaniya suka kwace su.

DUBA WANNAN: IG da INEC sun gaza shawo kan hargitsi tsakanin APC da PDP yayin taron masu ruwa da tsaki a Ekiti

“Ya yi kokarin guduwa amma sai jama’a suka fi karfinsa kuma nan take shi ma suka kashe shi kamar yadda ya kashe mahaifiyar matar sa.

Da yake tabbatar da afkuwar lamarin, kakakin ‘yan sanda na jihar Kebbi, DSP Mustapha Suleiman, ya bayyana cewar mazauna kauyen sun tsere daga gidajensu lokacin da jami’an hukumar ‘yan sanda suka isa kauyen.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel