Zaben Ekiti: Jami’an tsaro sun bankado masu buga kayan zaben karya

Zaben Ekiti: Jami’an tsaro sun bankado masu buga kayan zaben karya

A farkon makon nan ne mu ka samu labari cewa Jami’an ‘Yan Sandan Najeriya da ke Legas sun kai farmaki wani kamfanin buga takardu inda su ka iske ana buga kayan zabe na bogi.

Mutum 2 sun shiga hannun ‘Yan Sanda bayan da aka yi rama da su a cikin wani Kamfani mai suna O’Naphtali da ke Unguwar Gbagada a cikin Legas. Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Legas ne ya tabbatar da wannan.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Legas din CP Imohimi Edgal ya tabbatar da cewa sunan wanda yake da wannan kamfani da aka kama Eniola Fayose. A takaice dai mai kamfanin Takwaran Gwamnan Jihar Ekiti ne.

KU KARANTA: Minista Buhari ya nemi Jama’an Ekiti su zabi PDP.

Wannan abin dai ya kawo ce-ce-ku-ce kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar The Cable. Wasu na ganin cewa Eniola Fayose da kuma Gwamnan na Jihar Ekiti watau Mista Ayodele Peter Fayose ‘yan uwan juna ne.

Yanzu haka dai Gwamna Ayodele Fayose ya kammala wa’adin sa inda yake shirin kakaba Mataimakin sa Kolapo Olusola a matsayin sabon Gwamnan Jihar ya gaje shi a karkashin Jam’iyyar PDP a zaben da za ayi bana.

Dazu kun ji labari cewa wani babban ‘Dan Jam’iyyar APC a Jihar Ekiti Babafemi Ojudu yayi ikirarin cewa Gwamnan Jihar Ayo Fayose na kokarin hana Shugaba Buhari shigowa cikin Ekiti.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kwararren ‘Dan Najeriya ya samu aiki mai tsoka a Amurka

Kwararren ‘Dan Najeriya ya samu aiki mai tsoka a Amurka

Injiniyan Najeriya ya kafa tarihi bayan ya samu aiki da Apple
NAIJ.com
Mailfire view pixel