Kiyayewar Allah: dakarun soji sun kashe wutar wani rikicin kabilanci da ya so barkewa a jihar Gombe

Kiyayewar Allah: dakarun soji sun kashe wutar wani rikicin kabilanci da ya so barkewa a jihar Gombe

A yau, Litinin ne, runduna ta 301 ta dakarun sojin Najeriya ta dakile wani rikicin kabilanci da ya so barkewa tsakanin kabilun karamar hukumar Biliri da na Shongom a jihar Gombe.

Dakarun sojin sun gaggauta dira yankin bayan samun labarin abinda ke faruwa na tashin tarzoma tsakanin mutanen Bilir da na Shongom a kan rikicin iyaka.

Sanarwar da hukumar sojin ta fitar tab akin darektanta na yada labarai, Birgediya Janar Texas Chukwu, ta bayyana cewar jami’an sojin sun yi nasara cafke mutane 10 dake da hannu cikin yunkurin tayar da rikicin.

Kiyayewar Allah: dakarun soji sun kashe wutar wani rikicin kabilanci da ya so barkewa a jihar Gombe
Mutane 10 da aka kama a wani rikicin kabilanci da ya so barkewa a jihar Gombe

Daga cikin makamai da aka samu tare da mutane 10 da aka kama akwai; bindiga, samfurin AK47 da zagayen alburushi 28, wata bindigar, samfurin G3 da zagayen alburushi 21 cikinta, wata bindiga mai baki biyu, bindigun gida 10, wukake 3, layu, guraye da ragowar wasu makamai.

DUBA WANNAN: Labari mai dadi: An sake gano man fetur kwance makil a wani kauyen arewacin Najeriya

Hukumar soji ta bukaci jama’a da suke gaggauta sanar da hukuma duk wani tarnaki da kan iya rikidewa zuwa rikici domindaukan mataki a kan lokaci.

A kwanakin baya ne wani rikicin kabilanci ya barke a jihar Filato tare da yin sanadaiyar salwantar rayuka fiye da 200.

Tuni dai dama jihohin Benuwe da Taraba ke fama da rigingimu masu nasaba da kabilanci tsakanin manoma da makiyaya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel