Yanzu Yanzu: Buratai ya mika mambobin kungiyar Boko Haram 184 ga majalisar dinkin duniya

Yanzu Yanzu: Buratai ya mika mambobin kungiyar Boko Haram 184 ga majalisar dinkin duniya

Shugaban hafsan soji, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai zai mika yan ta’addan Boko Haram 184 ga jami’an majalisar dinkin duniya a ranar Litinin, 9 ga watan Yuli.

Za’a gudanar da taron mika su ne a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, Daily Sun ta ruwaito.

Kwanan nan majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa yaki da Boko Haram bai kare ba.

Wakilin babban sakataren majalisar dinkin duniya na musamman akan yankin Afrika ta yamma (UNOWAS), Dr Mohammed Ibn Chambers yace: “Ba’a gama da yan ta’addan Boko Haram ba zai dai an raunata su. Akwai bukatar a cigaba day akin.”

Yanzu Yanzu: Buratai ya mika mambobin kungiyar Boko Haram 184 ga majalisar dinkin duniya

Yanzu Yanzu: Buratai ya mika mambobin kungiyar Boko Haram 184 ga majalisar dinkin duniya

Chambers ya bayyana cewa majalisar dinkin duniya da kasashen waje za su cigaba da bayar da goyon bayansu don ganin an kakkabe yan ta’addan Boko Haram a tafkin chadi.

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa, a ranar Lahadi, fadar shugaban kasa tace tana dauke da hujjoji dake nuni ga cewa wasu yan siyasa ne ke da hannu a kashe-kashen da ake zargin makiyaya da aikatawa a yankunan kasar.

KU KARANTA KUMA: Ba za mu barwa bayinmu APC ba – Shugaban R-APC

Ta ce wasu yan siyasa da ba’a ambaci sunayensu bane ke amfani da yan ta’adda wajen aiwatar da kashe-kashen.

Babban mai ba shugaban kasa shawara a kafofin watsa labarai da shafukan zumunta, Garba Shehu ya bayyana hakan a wata sanarwa a Abuja.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kwararren ‘Dan Najeriya ya samu aiki mai tsoka a Amurka

Injiniyan Najeriya ya kafa tarihi bayan ya samu aiki da Apple

Injiniyan Najeriya ya kafa tarihi bayan ya samu aiki da Apple
NAIJ.com
Mailfire view pixel