‘Yan uwa 2 sun fada tarkon masu garkuwa da mutane, an nemi Naira miliyan N15m kudin fansa

‘Yan uwa 2 sun fada tarkon masu garkuwa da mutane, an nemi Naira miliyan N15m kudin fansa

- Masu garkuwa da mutane na cigaba da cin karensu ba babbaka

- Yanzu haka sun sace wasu 'yan uwa biyu har sun nemi fansa

A hutun karshe makon nan ne wasu masu garkuwa da mutane suka sace wasu 'yan kasuwa yan gida daya masu suna Alhaji Busari Olusa da kuma Saka Olusa mazauna unguwar Ajowa-Akoko da ke karamar hukumar Akoko ta Arewa da ke jihar Ondo.

Wata majiya ta tabbatar da cewa lamarin ya faru ne akan titin Akunu-Ajowa, inda aka sace su tare da barin mottarsu a gurin.

‘Yan uwa 2 sun fada tarkon masu garkuwa da mutane, an nemi Naira miliyan N15m kudin fansa
‘Yan uwa 2 sun fada tarkon masu garkuwa da mutane, an nemi Naira miliyan N15m kudin fansa

Bayan faruwar lamarin ne sai masu garkuwar su ka kirawo dangin wadanda aka sace din, kuma su ka bukaci kudin fansa kimanin Naira N15m, matukar suna bukatar a sakar musu 'yan uwan nasu.

Wannan Al'amarin ya jefa al'ummar wannan yankin cikin firgici da tsorata, in da su ka fara azumin kwana 3 tare da yin adduar Allah ya kawo karshen lamarin.

KU KARANTA: Na baiwa mahaifiyata Naira 50,000 a cikin kudin da muka yi fashinsu - inji wani dan fashi

Wannann Yana zuwa ne kwana biyu da yin garkuwa da matar wani basarake tare da direbansa a yankin.

A nasa bangaren jami'ain yan sandan mai kula da yankin Akoko Muhammed Maye, ya tabbatar da afkuwar lamarin. Sannan ya kuma kai ziyara inda lamarin ya faru. Shi ma mataimakin kwamishinan yan sanda Mai kula da shiyyar Akokon Razak Rauf,yaa tabbatar da cewa 'yan sanda za su hada kai domin magance matsalar tare kuma da ganin an sakko wadanda aka yi garkuwar da su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel