Buhari zai gyarawa Arewa manyan tituna a Jigawa da Kano

Buhari zai gyarawa Arewa manyan tituna a Jigawa da Kano

- Gwamnatin Tarayya za ta buda titin Kano zuwa Shuarin

- Wannan babbar hanya da ta ratsa wudil za ta ci Biliyan 5

- Hanyar ta hada Arewa maso Yamma da Arewa ta Gabas

Mun samu labari a makon nan cewa Gwamnatin Shugaba Buhari za ta yi wasu ayyuka a Arewacin Najeriya a wannan shekarar. Aikin da Gwamnatin Tarayyar za tayi zai ci kudi ne Naira Biliyan 5.

Buhari zai gyarawa Arewa manyan tituna a Jigawa da Kano

Ministan ayyuka da harkar wuta da gidaje a Najeriya

Kwanakin baya idan ba ku manta ba Gwamnatin Buhari ta kasafta wasu kudi na Sukuk da za a kashe a kowane Yanki na Kasar. An dai raba Naira Biliyan 100 ne ga kowane bangare inda kowa zai samu sama da Naira Biliyan 16.

KU KARANTA: Wasu Fasinjojin jirgi sun yi ido biyu da walakiri a Kano

A cikin wannan kudi ana sa rai Gwamnatin Tarayyar za ta buda titin Kano zuwa Maiduguri. Wannan hanya ce ta hada Jihar Kano da Jigawa da kuma Bauchi zuwa Jihar Yobe da Borno da ke Arewawa maso Gabashin kasar.

Wannan hanya da za a buda ita ce bangaren hanyar Kano zuwa Garin Wudil har zuwa Garin Shuarin wanda ke cikin Jihar Jigawa. Wannan babban aikin da za ayi kamar yadda mu ka samu labari zai lashe kudi Naira Biliyan 5 ne.

Kwanaki kun ji cewa Majalisar Dattawan Najeriya na nema a kafa wata Jami’a ta musamman ta ilmi a Jihar Kaduna da ke Arewacin kasar. Yanzu har maganar tayi nisa a Majalisar Dattawan kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kwararren ‘Dan Najeriya ya samu aiki mai tsoka a Amurka

Kwararren ‘Dan Najeriya ya samu aiki mai tsoka a Amurka

Injiniyan Najeriya ya kafa tarihi bayan ya samu aiki da Apple
NAIJ.com
Mailfire view pixel