Dogara ya bayyana abu daya tilo da zai iya kawo karshen rikicin jam’iyyar APC

Dogara ya bayyana abu daya tilo da zai iya kawo karshen rikicin jam’iyyar APC

Kakakin majalisar wakilai ta kasa, Yakubu Dogara, ya gargadi APC cewar adalci ne kadai zai iya magance rikicin da jam’iyyar ke fama da shi.

A wani jawabi da Turaki Hassan, kakakin Dogara ya aikewa da jaridar Premium Times a yau, Alhamis, bayan wata ganawa tsakanin sabon shugabancin APC da ‘yan majalisar ta wakilai, ya bayyana cewar idan ba adalci aka tabbatar ba rikicin jam’iyyar ba zai magantu ba.

Dogara ya bayyana abu daya tilo da zai iya kawo karshen rikicin jam’iyyar APC

Dogara

A yau ne sabon shugabancin jam’iyyar APC karkashi shugabanta na kasa, Adams Oshionhole, ya ziyarci majalisar ta wakilai domin ganawa da kuma sasanta rigingimu da jam’iyyar ke fama da shi.

DUBA WANNAN: Rikedewar nPDP zuwa rAPC: APC ta nesanta Buba Galadima da jam'iyyarta, ta ce ba ta da wani tsagi

Wasu rahotanni da suka dade suna yawo a kafafen yada labarai shine; wasu jiga-jigan ‘ya’yan APC da suka tsallako daga PDP gabanin zaben shekarar 2015 na shirin ficewa daga jam’iyyar bisa zargin nuna masu wariya da banbanci.

Wasu rahotannin ma sun bayyana cewar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya fice daga jam’iyyar APC.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Aisha Buhari ta halarci taron matan shugabannin Afrika (hotuna)

Aisha Buhari ta halarci taron matan shugabannin Afrika (hotuna)

Aisha Buhari ta halarci taron matan shugabannin Afrika (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel