An gurfanar da wani basarake a gaban kuliya saboda magudin zabe

An gurfanar da wani basarake a gaban kuliya saboda magudin zabe

- An gurfanar da wani basaraken jihar Anambra a gaban alkalin wata babban kotun tarayya bisa zarginsa da hannu cikin magudin zabe

- An gurfanar da basaraken mai suna Igwe Peter Uyanwa ne gaban kotu bisa zarginsa da bayyana sakamakon zabe na bogi

- An ruwaito cewa shima dan takarar zabe ne kafin ya zama basarake

A jiya Laraba 4 ga watan Yuli, an gurfanar da wani basaraken kauyen Ukwulu a karamar hukumar Dunukofia a jihar Anambra, Igwe Peter Uyanwa a gaban babban kotun tarayya dake Awka bisa zarginsa da aikata magudin zabe.

Punch ta ruwaito cewa basaraken ya gabatar da sakamakon zabe na bogi mai lamba FHC/AWK/C/79/18 a zaben yankunan Anaocha/Dunukofia/Njikoka da aka gudanar a ranar 7 ga watan Disambar 2017.

An gurfanar da wani basarake gaban kuliya saboda magudin zabe

An gurfanar da wani basarake gaban kuliya saboda magudin zabe

DUBA WANNAN: Alhaki: Bayan fashin mota, ya yi hadari ya mutu a ciki garin tserewa

NAIJ.com ta gano cewa Uyanwa wanda ya zama basarake bayan zaben ya kasance dan takara a zaben da aka gudanar kuma ya yi amfani da sakamakon zabe na bogi inda ya ambata kansa a matsayin wanda ya lashe zaben.

A karar da aka karanta, an zargi Peter Anukwu Uyanwa na jam'iyyar PDP da amfani da kirkirar sakamakon zabe na bogi wanda ya gabatar dashi kuma aka tabbatar dashi a matsayin wanda ya yi nasara a zaben Sanata mai wakiltan yankunan Anaocha/Dunukofia/Njikoka a zaben ranar 7 ga watan Disambar 2014.

Laifin kuma ya ci karo da sashi na 2(c) na Miscellaneous Offences Act na dokar tarayyar Najeriya ta shekarar 2004.

An daga cigaba da sauraon karar zuwa ranar 31 ga watan Oktoba bayan basaraken ya musanta aikata laifin da ake tuhumarsa dashi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kotun Turai ta kama wasu ‘Yan Najeriya 2 da laifi a badakalar rijiyar mai

Kotun Turai ta kama wasu ‘Yan Najeriya 2 da laifi a badakalar rijiyar mai

Kotun Turai ta kama wasu ‘Yan Najeriya 2 da laifi a badakalar rijiyar mai
NAIJ.com
Mailfire view pixel