Jami’an hukumar Kwastam sun kama Motocin shinkafa guda 11 a jihar Kaduna

Jami’an hukumar Kwastam sun kama Motocin shinkafa guda 11 a jihar Kaduna

Jami’an hukumar kwastam sun kama motoci dai dai har guda goma sha daya akan hanyar Kano, Zari zuwa Kaduna dauke da haramtattun shinkafa das suka shigo da su ta barauniyar hanya, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Mataimakin kwanturolan Kwastam na yankin, Ekanem Wills ne ya bayyana haka a ranar Litinin, 2 ga watan Yuli, a garin Kaduna, inda yace; “Mun kama motoci kirar Golf guda takwas, da J5 guda uku, dukkaninsu dauke da shinkafa.”

KU KARANTA: Hikima: Yadda wani fasihin Yaro ya burge shugaban kasar Faransa da sana’arsa

Wills ya kara da cewa kowanne mota daga cikinsu na dauke da akalla buhunan shinkafa guda Arba’in zuwa Arba’in da biyar, sa’annan sun cafke direbobin dake safarar shinkafar, yayin da bincike yana cigaba da gudana.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito Wills yana bayyana irin kokarin da gwamnatin tarayya ke yi ma hukumar, inda yace gwamnati ta samar musu sabbin motocin aiki da zasu dinga sintiri a cikinsu, wanda yace hakan zai kara ma jami’an hukumarsu kwarin gwiwa.

A wani labarin kuma, gwamnatin tarayya ta bakin ministan harkokin noma, Audu Ogbeh ta bayyana cewa nan bada jimawa ba za ta kulle iyakar kasar Najeriya da duk wata kasar da ake shigo da shinkafa ta barauniyar hanyar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar NAIJ.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zan marawa duk wanda ya samu tikitin takarar shugaban kasa a PDP baya – David Mark

Zan marawa duk wanda ya samu tikitin takarar shugaban kasa a PDP baya – David Mark

Zan marawa duk wanda ya samu tikitin takarar shugaban kasa a PDP baya – David Mark
NAIJ.com
Mailfire view pixel