Muna maraba da dawowar yan sabuwar PDP - Lamido

Muna maraba da dawowar yan sabuwar PDP - Lamido

Yayinda yan Najeriya ke jiran hukuncin karshe da yan sabuwar PDP dake APC za su yanke, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya bayyana cewa suna maraba da dawowarsu PDP, inda ya bayyana a matsayin asalin gidansu.

Lamido, dan takarar kujerar shugaban kasa karkashin PDP, ya bayyana hakan a Sokoto yayinda yake amsa tambayoyi daga manema labarai a lokacin gangamin zabensa a jihar.

Abubakar Baraje ke jagorantar sabuwar PDP sannan kuma akwai sauran manan yan saiyasa irin su Bukola Saraki, shugaban majalisar dattawa; Yakubu Dogara, kakakin majalisar wakilai, da kuma Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal.

Lamido ya bayyana cewaa yana daga cikin gwamnoni bakwai da rashin amincewarsu PDP ya fara a matsayin rikicin yan’uwa.

Muna maraba da dawowar yan sabuwar PDP - Lamido
Muna maraba da dawowar yan sabuwar PDP - Lamido

A halin da ake ciki, tattaunawar ‘Yan nPDP da Jam’iyyar APC mai mulki yana cin lokaci don haka wasu daga cikin manyan ‘Yan nPDP su ka yanke shawaran tattarawa su bar APC gaba daya su koma Jam’iyyar PDP inda su ka fito.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya nuna tsantsar soyayya ga yan Igbo – Rochas Okorocha

Ganin irin tafiyar hawainiyar da ake yi tsakanin ‘Yan nPDP karkashin shugabancin Alhaji Kawu Baraje, wasu daga cikin ‘Yan Jam’iyyar APC mai mulki sun kuma bangarewa a makon nan sun kafa wata kungiya mai suna ‘Reformed APC’.

Mun samu labari daga This Day cewa Tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da wasu manyan ‘Yan Majalisar kasar sun fice daga Kungiyar nPDP ganin maganar su Abubakar Kawu Baraje ta ki bullewa ga ko ina.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel