A karon faro Mikel Obi ya yi magana a kan tsaro a Najeriya bayan sace mahaifinsa

A karon faro Mikel Obi ya yi magana a kan tsaro a Najeriya bayan sace mahaifinsa

Kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Najeriya (Super Eagles) ya bayyana tsaro a Najeriya a matsayin abin tsoro bayan masu garkuwa sun sace mahaifinsa a karo na biyu.

A ranar 26 ga watan Yuni ne wasu masu garkuwa da mutane suka sace mahaifin Obi tare da direbansa bayan sun nuna masu bindiga.

An sanar da Obi batun sace mahaifin nasa sa’o’I hudu kafin wasan da Najeriya ta buga da kasar Argentina. Sannan an sako shi a jiya, Litinin.

“Wannan shine karo na biyu ana saka ni cikin firgici da tsoron rasa mahaifina,” Obi ya shaidawa sashen wasanni na BBC.

A karon faro Mikel Obi ya yi magana a kan tsaro a Najeriya bayan sace mahaifinsa
Mikel Obi

Jami’an rundunar Yansandan Najeriya sun sanar da ceto mahaifin dan wasan Super Eagles Mikel Obi daga hannun miyagun mutane masu garkuwa da mutane a ranar Litinin, 2 ga watan Yuli, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Kaakakin rundunar Yansandan jihar, SP Ebere Amaraizu ya bayyana cewar sun samu nasara ceto Dattijo Michael Obi ne da misalin karfe 2:30 na rana, tare da direbansa mai suna Ishaya John, a karshen wani kungurmin Daji, mai suna Dajin Udi dake jihar Enugu.

DUBA WANNAN: A karon farko bayan tsige Super Eagles, Ahmed Musa ya bayyana yadda ya ji

Mun samu labarin an sace Dattijo Michael Obi tare da direbansa ne a ranar 26ga watan Yuni akan hanyarsa Makurdi zuwa Enugu bayan ya fito daga garin Jos, inda aka neme su sama ko kasa aka rasa. Bayan wani dan lokaci sai yan bindigar suka fara kiran iyalansa a waya, suna neman kudin fansa miliyan goma".

Obi ya mika sakon godiya ga jami’an tsaro da mutanen Najeriya bisa gudunmawa da kulawar da suka nuna gare shi yayin iftila’in day a fada masa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel