Rashin tsaro zai zamo barazana ga zaben 2019 – Kungiyar CAN

Rashin tsaro zai zamo barazana ga zaben 2019 – Kungiyar CAN

Kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN, dake jihohi 17 na Kudanci kasar sun bayyana cewa matsalolin tsaro dake fadin kasar, musamman a yankin Arewa ta tsakiya babban barazana ne ga zaben 2019.

Kungiya CAN tace matsalar tsaro a yankin alamu ne na durkushewar tubalin tsaro a Najeriya.

Ta bayyana cewa da irin wannan hali da ake ciki, gudanar da zaben 2019 zai kasance babban matsala.

Kungiyar na martani ne akan cigaba da kashe-kashen sama da mutane 100 da ake zargin makiyaya da aikatawa ajihar Plateau.

KU KARANTA KUMA: Zanga-zangar yan sanda: Gwamnan Borno na ganawar sirri da Kyari

Sakataren kungiyar, Dr. Joseph Ajujungwa wanda yayi Magana ga manema labarai a Enugu yace kungiyar na cike da damuwa ganin cewa an kwashe kwanaki da dama da aikata wannan ta’assar amma ba’a dauki matakin kama wadanda suka aikata barnan ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai ya koka da tafiyar APC

Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai ya koka da tafiyar APC

Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai ya koka da tafiyar APC
NAIJ.com
Mailfire view pixel