Da dumi dumi: Yan bindiga sun bude ma jami’an Yansanda wuta a Abuja, sun kashe 7

Da dumi dumi: Yan bindiga sun bude ma jami’an Yansanda wuta a Abuja, sun kashe 7

Wasu gungun yan bindiga sun bude ma wasu jami’an Yansanda wuta a babban birnin tarayya Abuja, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar Yansanda guda bakwai daga cikinsu, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito wannan lamari ya faru ne daren Litinin, 2 ga watan Yuli, a shataletalen Galadimawa na garin Abuja, a yayin da yan bindigar dake cikin Mota suka sauke gilasan windunan motar, suke yi ma Yansanda ruwan harsashi, bakwai suka mutu, guda na cikin mawuyacin hali.

KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da mahaifin Mikel Obi

Sai dai Kaakakin rundunar Yansandan garin Abuja, Anjuguri Manzah bai amsa kiran da majiyamu ta yi masa ba don jin ta bakinsa game da wannan mummunan hari a garin Abuja.

Wutar lantarki ta aika da wani mutumi lahira yayin da yake kokarin satar wayoyin lantarki

Gawarwakinsu

A iya cewa wannan shi ne hari irinsa na farko da aka kaiwa babban birnin tarayya Abuja, tun bayan harin da Yan Boko Haram suka kai ofishin majalisar dinkin Duniya, da kuma babban ofishin Yansandan Najeriy, duk a garin Abuja.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar NAIJ.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jama’a na ganin Shugaba Buhari zai yi nasara a zabe mai zuwa

Mutane sun ce babu wanda zai ja da Shugaba Buhari a 2019

Jama’a na ganin Shugaba Buhari zai yi nasara a zabe mai zuwa
NAIJ.com
Mailfire view pixel