An hurowa Shugaba Buhari wuta ya tsige manyan Sojojin Najeriya

An hurowa Shugaba Buhari wuta ya tsige manyan Sojojin Najeriya

Labari na yawo cewa a halin yanzu jama’a da wasu Kungiyoyi masu zaman-kan su sun hurowa Shugaban kasa Muhammadu Buhari wuta ya tsige manyan Sojojin kasar saboda kashe-kashen da ya ki ci ya ki cinyewa a Najeriya.

An hurowa Shugaba Buhari wuta ya tsige manyan Sojojin Najeriya

Wasu sun yi kira a sauya Hafsun Sojojin Najeriya saboda rashin tsaro

Daga cikin wadanda su ka yi kira a sallami shugabannin Jami’an tsaron kasar akwai:

1. Jam’iyyar SDP

Jam’iyyar ta SDP ta bakin Sakatare-Janar din ta Princess Goldba Tolofari ta nemi Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sallami Shugabannin Hafsun Soji a huta domin a kawo karshen kashe-kashen da ake yi a kasar.

KU KARANTA: Sufetan 'Yan Sandan Najeriya ya amsa kiran Shugaban kasa

2. Dino Melaye

Sanatan Jam’iyyar APC Dino Melaye shi ma ya nemi Shugaban kasar ya fatattaki Hafsun Sojojin Najeriyar idan har ba za su iya aikin su ba. ‘Dan Majalisar ya goyi bayan wannan kira ne ta wani jawabi da yayi kwanan nan a Garin Lokoja.

3. Aminu Tambuwal

Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya fito yayi magana game da sha’anin tsaron kasar da ya lalace. Gwaman yace ya kamata Buhari yayi wani abu game da yadda Hafsun Sojojin Kasar ke aiki ko kuma a kawo wasu dabam su canje su.

Dazu kun ji cewa Kungiyar Miyetti Allah Kautal sun bayyana cewa duk mai kiran a tsige Hafsun Sojojin Kasar nan duk da kokarin da su ke yi bata-gari ne cikin ‘Yan siyasa ko wasun su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jam'iyyar PDP ne neman a tsige Sanatanta da ya sauya sheka zuwa APC

Bayan ya sauya sheka zuwa APC, PDP ne neman tsige Sanata Akpabio

Bayan ya sauya sheka zuwa APC, PDP ne neman tsige Sanata Akpabio
NAIJ.com
Mailfire view pixel