An daure mai daurewa: An kama gandiroba da laifin aikata fashi da makami

An daure mai daurewa: An kama gandiroba da laifin aikata fashi da makami

- Hukumar 'yan sanda reshen jihar Enugu tayi bajakolin wani ma'aikacin hukumar kula da gidajen yari ta kasa, Collins Ugwu, bayan samunsa da laifin aikata fashi da makami

- Ugwu, mai mukamin mataimakin sufuritanda, dan asalin karamar hukumar Ezza ta jihar Ebonyi ne kuma yana aiki ne a Abuja

- An kama Ugwu tare da wasu mazauna Abuja; Ifeanyi Ozor dan asalin jihar Enugu da Osetu Smart Agwa dan asalin jihar Imo

Hukumar 'yan sanda reshen jihar Enugu tayi bajakolin wani ma'aikacin hukumar kula da gidajen yari ta kasa, Collins Ugwu, bayan samunsa da laifin aikata fashi da makami.

Ugwu, mai mukamin mataimakin sufuritanda, dan asalin karamar hukumar Ezza ta jihar Ebonyi ne kuma yana aiki ne a Abuja.

An daure mai daurewa: An kama gandiroba da laifin aikata fashi da makami

Gidan yari a Najeriyai

An kama Ugwu tare da wasu mazauna Abuja; Ifeanyi Ozor dan asalin jihar Enugu da Osetu Smart Agwa dan asalin jihar Imo.

Wadanda ake zargin sun kware ne wajen yiwa masu hada-hada da harkoki a bankuna fashi ta hanyar yi masu labe da kula zirga-zirgar su.

DUBA WANNAN: Mata da ‘ya’yan wani dan sanda sun bawa ‘yan ta’adda kwangilar kashe shi

Hukumar 'yan sanda ta bayyana cewar, Ugwu da abokansa na amfani da wasu kayayyaki domin bude motar mutane tare da yashe masu kudin da suka ajiye.

Kazalika su kan damfari 'yan kasuwa ta hanyar sayen kaya tare da biyansu kudi ta hanyar tura sakon a-lat din banki na bogi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Babban sufetan Yansanda ya canza ma rundunar Yansandan SARS suna, karanta

Sufetan Yansanda ya kaddamar da garambawul ga rundunar SARS bisa umarnin Osibanjo

Sufetan Yansanda ya kaddamar da garambawul ga rundunar SARS bisa umarnin Osibanjo
NAIJ.com
Mailfire view pixel