Garin dadi na nesa: labarin wani gari da ba a sata, babu barawo kuma babu Dansanda

Garin dadi na nesa: labarin wani gari da ba a sata, babu barawo kuma babu Dansanda

Kai jama’a, wata miyar sai a makota, na kara muku da garin dadi na nesa, wai inji angulu da ta leka masai, kwatankwacin haka ne ya faru a wata kasa dake gabashin nahiyar Turai, watau Romaniya, inda aka samu wani gari a kasar da aka kwashe sama da shekaru 20 ba a taba sata ba.

Mai karatu kada ka yi mamaki, wai don ana yawan samun yan fashi da makami, yan sane, da kuma masu garkuwa da mutane a inda kake, ba zai hana a samu inda ba su da matsalar sata, ko ta sane ba, ko kuma ta yan fashi da makami ba.

KU KARANTA: Abinda ya kamata kuyi idan har kuna son kama Shekau cikin ruwan sanyi – Kwamandan Boko Haram ga Sojoji

Garin dadi na nesa: labarin wani gari da ba a sata, babu barawo kuma babu Dansanda
Garin

A garin Eibenthal, wani gari dake yammacin kasar Romaniya, an kwashe shekara da shekaru basu taba kama barawo ba, kuma ba a taba samun labarin an satar ma wani ko anini ba! Kai lamarin wannan kasa ya ta’azzara har ta kai ga suna rataye jakar kudi akan hanya, kuma babu mai tabasu ko ba jima, ko ba dade.

Garin dadi na nesa: labarin wani gari da ba a sata, babu barawo kuma babu Dansanda
Garin

Shi dai wannan gari yana kan dutsen Banatuli ne, cikin karamar hukumar Mehedinti, kuma ya kunshi jama’atr kabilar Czech ne, shi ne garin da babu ofishin Yansanda, kuma babu jami’an tsaro, amma mazauna garin na zaune cikin cikakkiyar kwanciyar hankali ba tsoro ba fargaba.

Wannan gari ya yi suna wajen sayen burodi, don haka yan gari suke ajiye kudin burodinsu akan hanya, ta yadda idan mai burodin ya zo, sai ya ajiye ma kowa burodinsa ya dauki kudinsa yayi gaba, inda kuma da canji, sai u hada burodin da canjin su rataye musu abinsu, tun a shekarar 1996 ake wannan al’ada, ba’a taba samun rahoton bacewar kudi ko burodi ba.

Garin dadi na nesa: labarin wani gari da ba a sata, babu barawo kuma babu Dansanda
Garin

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wani Fasto a garin mai suna Baclab Masek yana cewa yana da kadarori da dama a kofar gidansa, kuma babu ko daya daga cikinsu da ya taba ciwon kai, “A shekaru goma sha uku da na kwashe ina wa’azi a garin nan ban tana jin labarin barawo ya yi sata a garin nan ba.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel