Boko Haram: Shekau bashi da lafiya, yana cikin mawuyacin hali

Boko Haram: Shekau bashi da lafiya, yana cikin mawuyacin hali

Wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na AFP ya wallafa ranar juma’a ya tabbatar da cewar shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, na can kwance ba lafiya, cikin mawuyacin hali.

Majiyar AFP ta shaida masu cewar Shekau na fama da cututtuka da dama da suka saka shi yin laushi tare da hana shi cigaba da gudanar da shugabancin kungiyar Boko Haram. Wasu daga cikin cututtukan da majiyar ta lissafa sun hada da; hawan jini, dusashewar gani da kuma ciwan suga da sauran su.

Wata majiya, dab a ta yarda a ambaci sunanta ba, daga cikin jami’an tsaro ta tabbatar da cewar ciwon suga na matukar wahalar da Shekau.

Boko Haram: Shekau bashi da lafiya, yana cikin mawuyacin hali
Mahifiyar Shekau

Yana fama da dusashewar gani dake barazanar cinye masa idanu sakamakon matsanancin ciwon suga da yake fama da shi,” a cewar majiyar.

Majiyar, dake da masaniyar harkokin kungiyar Boko Haram, ta sanar da cewar manyan kwamandojin Boko haram sun magantu a kan halin da yake ciki tare da gudanar da taro domin nemawa kungiyar mafita ta fuskar shugabanci.

DUBA WANNAN: Rikicin jihar Filato: Muna sane sarai da abinda ake son kullawa - CAN

Wasu masana sun bayyana cewar, rashin lafiyar Shekau zata bayar da dammar yin sulhu da Boko Haram domin tun farko tsaginsa ne ya ki yarda da sulhun.

Shekau kan yawaita sakin faifan bidiyo lokacin da Boko Haram ke cin karensu babu babbaka. Saidai tun bayan faifan bidiyon day a fitar a ranar 6 ga watan Fabrairu, Shekau bai kara fitowa a cikin faifan bidiyo ba.

Sau uku gwamnatin Najeriya na ikirarin kashe Shekau amma sai a gan shi cikin sabon faifan bidiyo yana karyata hakan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel