2019: Ana sa ran matasa da yawa za su yi takara - Saraki

2019: Ana sa ran matasa da yawa za su yi takara - Saraki

Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya bayyana cewa ana sanya ran matasa da yawa za su fito takara a zaben 2019 sakamakon sanya hannu da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a dokar ba matasa damar shiga siyasa.

Ya yi Magana ne a ranar Juma’a a Abuja wajen bikin murnar amincewa da dokar ba matasa damar yin siyasa.

Saraki wanda ya samu wakilcin hadiminsa, Kinsley Amaku ya bayyana matasan Najeriya a matsayin masu son cigaban dimokradiyya.

2019: Ana sa ran matasa da yawa za su yi takara - Saraki

2019: Ana sa ran matasa da yawa za su yi takara - Saraki

Shugaban majalisar dattawan ya yi murnar wannan cigaban inda ya bayyana cewa hakan zai ba matasa da dama shiga harkar siyasa a zaben 2019.

KU KARANTA KUMA: Har yanzu Kwankwaso na jam’iyyar APC – Jigon jam’iyyar

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa dan takarar shugabancin kasa karkashin lemar Peoples Democratic Party (PDP), Dr Datti Baba-Ahmed, ya fada ma jam’iyyar cewa su bashi tikitin takarar shugabancin kasa, cewa zai kora shugaban kasa Muhammadu Buhari gida a zaben shekara mai zuwa.

Ya bayyana hakan ne sakatariyar jam’iyar ta kasa dake Abuja lokacin da ya je kaddamar da kudirinsa na tsayawa takara a ranar Juma’a.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku bide mu a shafukanmu na kafofin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Buhari na Samun Matsin Lamba Daga makusantanshi akan Mayarda Lawan Daura Shugaban DSS

Buhari na Samun Matsin Lamba Daga makusantanshi akan Mayarda Lawan Daura Shugaban DSS

Buhari na Samun Matsin Lamba Daga makusantanshi akan Mayarda Lawan Daura Shugaban DSS
NAIJ.com
Mailfire view pixel