EFCC ta gurfanar da wani Tsohon Minista da wasu Mutane 4 bisa laifin Almundahana

EFCC ta gurfanar da wani Tsohon Minista da wasu Mutane 4 bisa laifin Almundahana

A ranar Alhamis din da ta gabata hukumar hana yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC, ta gurfanar da wani Ministan Kimiyya da Fasaha a gaban Kuliya, Dr. Abdu Bulama, bisa laifin almundahanar dukiya karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Jonathan.

Hukumar a reshen ta dake birnin Maiduguri, ta gurfanar da tsohon ministan ne tare da wasu mutane hudu a gaban babbar kotun tarayya dake babban birnin Damaturu na jihar Yobe bisa aikata laifin almundahanar makudan dukiya.

Sauran wadanda hukumar ta gurfanar a gaban kuliya sun hadar da tsohon shugaban jam'iyyar PDP na jihar, Alhaji Abbagana Tata, Honarabul Muhammad Kadai, Muhammad Mamu da kuma Hassan Ibn Jaks.

EFCC ta gurfanar da wani Tsohon Minista da wasu Mutane 4 bisa laifin Almundahana
EFCC ta gurfanar da wani Tsohon Minista da wasu Mutane 4 bisa laifin Almundahana

Kamar yadda hukumar ta EFCC ta bayyana, ana zargin wannan mutane biyar da laifin almundahanar dukiya ta sama da Naira Miliyan 229, wanda wannan laifi ya sabawa sashe na 18 cikin dokoki na laifukan kudi

Legit.ng ta fahimci cewa, a halin yanzu ana sauraron kotu ta sanya ranar fara sauraron shari'ar sakamakon rashin amsa laifin da ake zargin wannan mutanen suka aikata.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya rattaba hannu kan wasu sabbin Dokoki 2 a Najeriya

Alkalin kotun, Hamada Isa Dashen, ya hau kujerar naki dangane da neman beli da wannan mutane suka nema, inda ya bayar da umarnin hukumar EFCC ta ci gaba da tsare su a katarar ta.

Rahotanni kamar yadda shafin jaridar The Nation ya bayyana, lauyoyi masu tuhuma da kariya sun gudanar da yarjejeniya a tsakanin su ta fara sauraron karar a ranar 24 ga watan Satumba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel