Tuna baya: Takaitaccen tarihin sadauki, Hassan Sarkin Dogarai

Tuna baya: Takaitaccen tarihin sadauki, Hassan Sarkin Dogarai

Hassan Adamu, da aka fi sani da Hassan sarkin Dogarai, shine sarkin Dogarai na uku da marigayi sarkin Kano, Ado Bayero ya nada a mastayin shugaban dogaran sarki a shekarar 1990.

Kafin nadin Hassan a matsayin sarkin dogaran fadar Kano, Marigayi Ado ya nada wasu mutane biyu a baya; Dan-Wudil da Adamu, kuma bayan mutuwar Adamu ne aka nada Hassan, sannan shi ma bayan mutuwarsa aka nada sarkin Dogarai na yanzu, Danbala.

Saidai sabanin sarkin dogarai Adamu da Dan-Wudil, Hassan ba bafade bane. Asalinsa direba ne dake sana’ar tuka mota kafin daga baya ya zama hadimi ga galadiman Kano, Marigayi Tijjani Hashim, mutumin da ya fara nada shi a matsayin shamakinsa kuma ya zama silar shigar sa cikin fadar Kano.

Tuna baya: Takaitaccen tarihin sadauki, Hassan Sarkin Dogarai
Hassan Dogarai

A shekarar 1990 ne, bayan mutuwar sarkin Dogarai Dan-Wudil, Marigayi Hashim ya roki sarkin Kano Ado alfarmar ya nada Hassan a matsayin sarkin Dogarai saboda tsananin biyayyar sa da kuma jarumtar sa, sannan ga soyayya da yake nunawa ga sarkin.

Marigayi Hassan na zaune ne da iyalinsa a unguwar Sagagi, kusa da gidan mahaifiyar Ado Bayero, kafin daga bisani ya koma unguwar gidan sarkin Dogarai dake unguwar Dogarai, daf da gidan sarkin Kano.

Hassan ya yi shura a cikin sarakunan Dogaran Kano saboda karfi da jarumta da kuma tsananin biyayyarsa ga sarkin Kano Ado.

DUBA WANNAN: Kalli hotuna: Kwankwaso ya ziyarci Fayose a Ekiti, ya yiwa dan takarar PDP kamfen

Hassan sarcecen mutum ne, saboda girma da tsayinsa har kirari ake yi masa da Bishiya.

Wani dan asalin unguwar Dogarai, Ibrahim Mu’azzam Sadauki, da ya san marigayi Hassan, ya shaidawa Legit.ng cewar, Marigayi Hassan ya fara haduwa ne da shahararren mawakin Hausa, Mamman Shata, yayin da yake sana’ar sa ta tuka mota. Bayan Hassan ya zama sarkin Dogarai ne, Shata ya rera masa wakar “Hassan sarkin Dogarai”, wakar da ta kara daukaka sunansa a Duniya.

Yanzu haka iyalan Hassan sun koma gidansa dake unguwar Sagagi inda suka cigaba da rayuwa bayan mutuwar mahaifinsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel