Wani Kwarto da kwartuwarsa sun fuskanci tsatstsauran hukunci a Jigawa

Wani Kwarto da kwartuwarsa sun fuskanci tsatstsauran hukunci a Jigawa

Wani Kwarto da wata Kwartuwa sun gamu da tsatstsauran hukunci daga wani Alkalin Kotun Shari’ar Musulunci sakamakon kamasu da laifin yunkurin aikata zina da tsakar rana alhali da aurensu, kamar yadda jaridar Aminiya ta ruwaito.

Wadanda abin ya shafa sune Abubakar Abdullahi da Magajiya Uba, dukkaninsu mazauna unguwar Danmasara dake garin Dutse, babban birnin jihar Jigawa, an kamasu ne a daidai lokacin da Kwarton ke lallaba kwartuwar don ta bashi hadin kai.

KU KARANTA: EFCC ta tasa keyar tsohon Minista gaban kuliya manta sabo kan wawurar N85,000,000

A yayin zaman shari’ar da aka yi, Dansanda mai kara ya kawo shaidu gaban Kotu, wadanda suka tabbatar da wadanda ake tuhumar sun aikata laifin da ake tuhumarsu da shi, haka zalika shi ma Abdullahi da Magajiya basu musanta laifin ba, inji rahoton majiyar Legit.ng.

Bayan kammala sauraron bangarorin masu kara da wadanda ake yi ma kara, Alkalin Kotun, Yusuf Ibrahim ya yanke musu hukuncin zaman gidan Yari na tsawo shekara dai dai, ko kuma zabin biyan tara kudi naira dubu goma kowannensu.

A wani labarin kuma, Alkali Yusuf ya daure wani mutumi mai suna Aliyu Malumawa bayan kama shi da laifin raunata wasu mutane biyu da adda yayin da ya zargesu da satar wayarsa, inda Alkalin ya umarceshi ya biyasu naira dubu arba’in don kulawa da kansu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel