Da dumi dumi: EFCC ta tasa keyar tsohon Minista gaban kuliya manta sabo kan wawurar N85,000,000

Da dumi dumi: EFCC ta tasa keyar tsohon Minista gaban kuliya manta sabo kan wawurar N85,000,000

Hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta tasa wani tsohon ministan kimiyya da fasaha a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan gaban Kotu kan zarginsa da handamar wasu makudan kudaden al’umma.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wannan tsohon Minista shi ne Dakta Abdu, kuma EFCC ta gurfanar da shi ne a gaban babbar kotun tarayya dake Damaturu na jihar Yobe, tare da wasu mutane hudu da ake zargin tare da suka yi wawura tare da handame kudi naira miliyan Tamanin da biyar.

KU KARANTA: Labarin wani Limami a garin Jos da ya boye Kiristoci a cikin Masallaci

An hallaka mutane guda 3 a wani harin da yan bindiga suka kai jihar Kogi

Abdu da jama'ansa

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito sunayen sauran mutane hudu kamar haka; Mohammed Kadai, Abbagana Tata, Muhamamd Mamu da Hassan Ibn Jaks, kuma ana tuhumarsu ne da laifin amsar kudin da suka haura iyaka ba tare da bin Banki ba.

Shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu ya bayyana cewa ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen yaki da rashawa da yake yi, inda yace idan har ba’a magance cin hanci da rashawa a Najeriya ba, toh matsalar za ta kar Najeriya nan gaba kadan.

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar NAIJ.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Mutane sun ce babu wanda zai ja da Shugaba Buhari a 2019

Mutane sun ce babu wanda zai ja da Shugaba Buhari a 2019

Jama’a na ganin Shugaba Buhari zai yi nasara a zabe mai zuwa
NAIJ.com
Mailfire view pixel