Gwamnonin Najeriya za su gana da Shugabannin tsaro na Kasa

Gwamnonin Najeriya za su gana da Shugabannin tsaro na Kasa

Mambobi na kungiyar gwamnonin Najeriya sun yanke shawarar ganawa da dukkanin shugabannin tsaro na kasa domin samar da matsaya guda ta magance barazana ta matsalolin tsaro da kasar nan take fuskanta.

Shugaban wannan kungiya, gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Abubakar Yari, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai bayan taron kungiyar da suka gudanar cikin birnin Abuja a ranar Alhamis din da ta gabata.

Gwamna Yari ya bayyana cewa, dukkanin gwamnonin kasar nan sun yi tir gami da Allah wadai dangane da haren-haren ranar Lahadin da ta gabata da suka afku a jihar Filato, inda suke kira kan gaggauta bankado wannan 'yan tadda domin su fuskanci hukunci.

Gwamnonin Najeriya za su gana da Shugabannin tsaro na Kasa

Gwamnonin Najeriya za su gana da Shugabannin tsaro na Kasa

A cewar Yari, gwamnonin sun yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da Mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo, dangane da ziyarar su cikin azama da suka kai domin jajantawa al'umma jihar Filato.

DUBA WANNAN: Gwamnatin jihar Oyo ta rufe Kasuwar Badija yayin da 'Yan sanda da Mahauta suka yi arangama

Hakazalika gwamnonin sun yabawa gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, dangane da yadda yake tafi da al'amurran jihar bayan afkuwar wannan hari.

Jaridar NAIJ.com ta kuma ruwaito cewa, Bankin Duniya zai malalo makudan kudade na $2.1bn domin gudanar da wasu muhimman ayyuka bakwai cikin kasar nan ta Najeriya domin bukasa tattalin arziki da kuma ci gaban ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Bayan kwanaki 9 yana bacci, mai garkuwa a mutanen da ya sha Tramol ya sheka lahira

Bayan kwanaki 9 yana bacci, mai garkuwa a mutanen da ya sha Tramol ya sheka lahira

Bayan kwanaki 9 yana bacci, mai garkuwa a mutanen da ya sha Tramol ya sheka lahira
NAIJ.com
Mailfire view pixel