Kotu ta kwace wani Fuloti na N325.4m mallakin Tsohuwar Ministan man Fetur, Diezani

Kotu ta kwace wani Fuloti na N325.4m mallakin Tsohuwar Ministan man Fetur, Diezani

Mun samu rahoton cewa a ranar Larabar da ta gabata ne babbar Kotun tarayya dake jihar Legas, ta bayar da umarnin kwace wani katafaren Fuloti a unguwar Lekki ta jihar Legas mallakin tsohuwar Ministan man fetur, Misis Diezani Alison-Madueke.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya bayyana, wannan babban fuloti mai lamba 13 a yankin Oniru na unguwar ta Lekki zai kai daraja da kimanin Naira Miliyan 325.4.

Kotu ta kwace wani Fuloti na N325.4m mallakin Tsohuwar Ministan man Fetur, Diezani
Kotu ta kwace wani Fuloti na N325.4m mallakin Tsohuwar Ministan man Fetur, Diezani

Kotun karkashin jagorancin Alkali Babs Kuewumi, ta bayar da umarnin kwace wannan kadara ta tsohuwar ministan sakamakon bukata ta hukumar hana yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC.

DUBA WANNAN: Sojin Najeriya sun yiwa 'Yan Boko Haram kwanton bauna, sun kwato Makamai da ceto Mutane 33 a Jihar Borno

Lauya mai wakiltar hukumar ta EFCC, Mista Anslem Ozioko, shine ya gabatar da kansa gaban Kotun a ranar Larabar da ta gabata da zargin tsohuwar Ministan kan mallakar Fulotin ta hanyar magudi.

Legit.ng ta fahimci cewa, bayan zartar da wannan hukunci alkali Kuewumi ya bayar da umarni ga hukumar ta EFCC kan wallafa wannan lamari a daya daga cikin manyan jaridun kasar nan domin sanar da suk wasu masu ruwa da tsaki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel