Buhari ya yi umurnin canza fasalin lamuran rundunar SARS ya sha alwashin kawo karshen ta’asa

Buhari ya yi umurnin canza fasalin lamuran rundunar SARS ya sha alwashin kawo karshen ta’asa

Biyo bayan zargin da ake yiwa na irin ta’asar da jami’an yan sandan SARS ke aikatawa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi umurnin cewa a gaggauta sake fasalin rundunar.

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya bayyana hakan a wata sanarwa day a saki a jiya ta hannun babban mai ba shugaban kasa shawara a kafofin sadarwa, na ofishin mataimakin shugaban kasa, Laolu Akande, yayinda yake maida martani ga wasu tambayoyi daga yan Najeriya, a babban dakin wani taro da aka gabatar a Ibadan, jihar Oyo.

Gwamnatin tarayya ta nuna damuwa kan ta’asa dabandaban da ake zargin jami’an da aikatawa sannan kuma ta sha alwashin magance matsalar nan ba da jimawa ba.

Buhari ya yi umurnin canza fasalin lamuan hukumar SARS ya sha alwashin kawo karshen ta’asa

Buhari ya yi umurnin canza fasalin lamuan hukumar SARS ya sha alwashin kawo karshen ta’asa

Osinbajo ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta jajirce don ganin ta magance wannan matsala game da yadda SARS ke tafiyar da ayyukansu, sannan kuma shugaba Buhari ya bayar da umurnin sake duba kan lamarin cikin gaggawa tare da yin garambawul a sashin.

KU KARANTA KUMA: Kisan Plateau: Masu zanga-zanga sun kai mamaya gidan gwamnati, sun lalata kayayyaki

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa Sabon rahoto da gidauniyar Reuters Foundation ta saki a ranar Talata, ya ambaci Najeriya a matsayin ta tara cikin kasashe mafi hatsari ga mata.

Najeriya ta shiga rukunin tare da Iniya wacce itace kan gaba a jerin kasashen, DR Congo, Saudiyya, Afghanistan, da kuma Somalia ta fannin lalata, tsubbu da kuma safarar mutane.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Bikin Sallah: Gwamna Tambuwal ya yiwa marayun Sakkwato sha tara na arziki

Bikin Sallah: Gwamna Tambuwal ya yiwa marayun Sakkwato sha tara na arziki

Bikin Sallah: Gwamna Tambuwal ya yiwa marayun Sakkwato sha tara na arziki
NAIJ.com
Mailfire view pixel