An sake kwatawa: An yi asarar rayuwar wasu kananan Yara guda 2 a sanadiyyar gobara

An sake kwatawa: An yi asarar rayuwar wasu kananan Yara guda 2 a sanadiyyar gobara

Kimanin awanni uku da faruwar gobarar wata Kasuwa dake garin Akure na jihar Ondo, an kara samun wata mummunan gobara da ta tashi a yankin Edo Lodge na jihar, wanda ta hallaka wasu kananan yara guda biyu yan gida daya, inji rahoton jaridar Vanguard.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito sunayen yaran kamar haka; Damilare Omolere mai shekaru hudu da Itunu mai shekaru biyu, suna karkashin kulawar yayarsu mai shekarau goma sha daya ne lokacin da mummunan lamarin ya auku, bugu da kari mahaifnsu ya yi tafiya, yayin da Uwarsu ta fita aiki.

Haka zalika, babbar yayartasu da aka bata kulawar yaran ta fice daga gida, ta bar yaran su kadai zaune a gida, inda ko a lokacin da ta dawo gida sai ta tarar da gawar yaran, tare da gidansu ya babbake tun daga sama har kasa.

KU KARANTA: Laftanar Janar Buratai ya kaddamar da madatsar ruwa da Sojoji suka gina a Yobe

Sai dai rahotanni sun bayyana cewar kyandir ne ya janyo wannan ibtila’I, wanda yayar yaran ta daura shi akan teburi, alhalin yana kunne da wuta, inda zake zaton ya fadi a kasa, sa wutar ta kama shimfidar dakin, daga wutar ya kama ci balbal.

A wani labarin kuma, wata yar kasuwar a jihar Ondo, guda cikin wadanda gobarar kasuwar ta lakume ma shaguna, Elizabeth Aina ta yanke jiki ta fadi bayan kwanaki hudu da faruwar gobarar, sakamakon barnar da gobarar ta yi mata.

Maigidan Aina mai suna, Jacob Aina ya tabbatar da mutuwar matar tasa, wanda yace suna da yaya biyar tare da marigayiyar, ya bayyana cewa Matartasa na da shaguna biyu a kasuwar, kuma dukkaninsu sun kone kurmus!

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel