Kiristoci sunyi zanga-zanga a Jos, kalli hotuna

Kiristoci sunyi zanga-zanga a Jos, kalli hotuna

Kiristoci da dama sunyi zanga-zanga a babban birnin Jihar Filato, Jos saboda nuna bacin ransu game da kashe-kashen da aka yi a wasu sassan jihar a ranar Lahadi da ta gabata.

Masu zanga-zangan sun mamaye titunan birnin Jos sanye da bakaken tufafi da kwalaye dauke da rubutu daban-daban masu bayyana irin abubuwan da ke damunsa a jihar tare da kira ga hukuma ta dauki mataki.

Rahottani da ya fito daga shugabanin yankunan da lamarin ya afku sun bayyana cewa rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 200 amma hukumar yan sanda ta ce mutane 86 ne suka rasu.

DUBA WANNAN: Rashin tausayi: Boko Haram sunyi wa mutane 7 yankan rago a kan neman itace

A dai yau ne Kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki suka garzaya jihar ta Filato don yin jaje ga al'ummar jihar bisa rashin da su kayi.

Kiristoci sunyi zanga-zanga a Jos, kalli hotuna
Kiristoci sunyi zanga-zanga a Jos, kalli hotuna

Shima shugaba Buhari ya ziyarci jihar ta Filato a jiya Talata 26 ga watan Yuni inda ya bayyana al'ummar jihar cewa gwamnatinsa tana iya kokarinta na ganin ta kare rayyuka da dukiyoyin al'umma a duk sassan kasar nan.

A bangarensa, gwamna Lalong na Jihar Filato ya ce wasu marasa ganin an zauna lafiya ne suka kai harin a jihar, ya kuma shaida wa mutanen jihar cewa gwamnatinsa za ta tabbatar da cewa an binciko wanda ke da hannu cikin harin don su fuskanci hukunci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel