Manyan dillalan wiwi guda 88 sun fada komar jami’an hukumar NDLEA

Manyan dillalan wiwi guda 88 sun fada komar jami’an hukumar NDLEA

Jami’an hukumar yaki da sha tare da ta’ammali da miyagun kwayoyi, NDLEA, sun kama manyan dillalan wiwi guda tamanin da takwas a jihar Kebbi a cikin watanni shidda na shekarar 2018, kamar yadda kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, ta ruwaito.

Kwamandan hukumar, reshen jihar Kebbi, Suleiman Jadi ne ya sanar da haka a ranar Talata, 26 ga watan Yuni a garin Birnin Kebbi, inda yace sun kama kilo 857.320 na tabar wiwi da sauran kayan maye daga hannun dillalan.

KU KARANTA: Yansandan Najeriya sun yi jarumta wajen tartwatsa gugun yan fashi da makami

Jadi ya bayyana haka ne a bikin ranar yaki da miyagun kwayoyi na majalisar dinkin Duniya, inda yace: “Rundunarmu na yaki tukuru da miyagun kwayoyi, a tsakanin watan Janairu da Yuni na bana, mun kwace kilo 857.320 na tabar wiwi da sauran kayan maye daga hannun mutane 88.”

Haka zalika yace Kotu ta kama daure dillalan wiwi su 23 tsawon shekaru daban daban a Kurkuku, yayinda sauran shari’u na cigaba da tafiya a babban kotun tarayya na jihar Kebbi, da wannan ne yayi kira ga iyaye su dinga lura da yanayin da yayansu ke ciki, kafin su fara shiga harkar shaye shaye.

Daga karshe yayi kira ga jama’a dasu dinga baiwa Yansanda bayanai da zasu taimaka musu a aikinsu, sa’annan yay aba da kokarin da uwargidar gwamnan jihar Kebbi, Zainab Bagudu ke yi na kawo karshen matsalar shaye shaye a jihar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar NAIJ.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kaico: Hatsarin Wata Babbar Mota ya muƙurƙushe wasu Motoci 15 a Arewacin Najeriya

Kaico: Hatsarin Wata Babbar Mota ya muƙurƙushe wasu Motoci 15 a Arewacin Najeriya

Kaico: Hatsarin Wata Babbar Mota ya muƙurƙushe wasu Motoci 15 a Arewacin Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel