An tura Rundunar musamman zuwa Jihar Filato bayan barkewan rikicin Barkin Ladi

An tura Rundunar musamman zuwa Jihar Filato bayan barkewan rikicin Barkin Ladi

- Sufetan ‘Yan Sanda ya aika Runduna guda zuwa Garin Jos domin kawo zaman lafiya

- Rikicin Makiyaya da ‘Yan wasu Kabila ne ya barke a Garin Filato a karshen makon can

- Mai magana da bakin ‘Yan Sanda Jimoh Moshood yace an aika Bataliya zuwa Yankin

Mun samu labari cewa Jami’an ‘Yan Sandan Najeriya sun shiga Garin Filato domin kawo zaman lafiya bayan rikicin da ya barke a cikin Garin Barkin Ladi a karshen makon da ya wuce.

An tura Rundunar musamman zuwa Jihar Filato bayan barkewan rikicin Barkin Ladi
Mai magana da yawun 'Yan Sandan Najeriya Jimoh Moshood

Jaridar mu ta samu labarin cewa an tura Rundunar tsaro na musamman zuwa Jihar Filato bayan barkewan rikicin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane da-dama. Mai magana da yawun Rundunar ‘Yan Sandan ya bayyana wannan.

KU KARANTA: Kai jama’a: Yadda wasu Musulmai su ka tsallake rijiya da baya a rikicin Filato

Jimoh Moshood wanda yayi magana a madadin Rundunar ‘Yan Sanda yace Sufeta Janar na Kasar Ibrahim Idris ya aika daya daga cikin Mataimakan sa DIG Joshiak Habila ya tada Jama’ar sa su tattara su wuce Garin Jos cikin gaggawa.

Joshiak Habila wanda shi ke kula da tsare-tsaren Rundunar zai tafi neda Jiragen yawo 2 da kuma manyan makamai da sauran kayan aiki. Bayan nan kuma an aika wata Runduna ta liken asiri da ‘Yan kwana-kwana na Jami’an tsaro zuwa Yankin.

Babban Jami’in ‘Yan Sandan Jimoh Moshood yace an kuma dauki ‘Yan Sanda da-dama daga sauran Jihohi domin maganin tarzomar da ta tashi a Jihar Filato. Kafin nan dai Mataimakin Shugaban Kasa da kan sa ya ziyarci Jihar Filaton.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel