Shugaba Buhari ya bayyana masu hannu a kasha-kashen jihar Filato, ya fadi abinda suke son cimma

Shugaba Buhari ya bayyana masu hannu a kasha-kashen jihar Filato, ya fadi abinda suke son cimma

A yau, Litinin, ne shugaba Buhari ya koka bisa kan yadda wasu ‘yan siyasa masu son zuciya suka wofantar da ran mutum domin kawai cimma manufar siyasa.

Shugaba Buhari na wannan kalamai ne tab akin kakakin sa, Garba Shehu, yayin da yake magana a kan kisan mutane a jihar Filato.

Malam Shehu ya bayyana cewar masu ingiza wutar wadannan rigingimu na yin hakan ne da tunanin zasu yi amfani da tashe-tashen hankula domin cimma manufofin siyasa a zaben shekarar 2019 mai zuwa.

Shugaba Buhari ya bayyana masu hannu a kasha-kashen jihar Filato, ya fadi abinda suke son cimma

Shugaba Buhari

Duk da mun san akwai matsaloli na tattalin arziki da zamantakewa a rikicin makiya da manoma, mun san akwai ‘yan siyasa dake kara rurar wutar rikicin da niyyar amfani da hakan a matsayin makamin yakin neman cin zabe,” a cewar Malam Shehu.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar, an kasha wa makiyaya shanu fiye da 100 a kwanakin baya amma gwamnan jihar, Simon Lalong, ya shiga batun tare da rokon dukkan kabilun yankin da abin ya faru da su yi hakuri tare da basu tabbacin cewar jami’an tsaro zasu shiga cikin lamarin. Amma ko sa’o’i 24 ba a yi ba sai rikici ya kara barkewa a jihar.

DUBA WANNAN: Kotu ta tsayar da ranar yanke hukunci a kan karar da Dasuki ya shigar da gwamnatin tarayya

Hakan ne ya bawa wasu batagarin ‘yan daba dammar yin amfani da rikicin domin aikata fashi da kuma kai wa abokan hamayyar siyasa hari.

A jiya, Lahadi, ne hukumar ‘yan sanda ta sanar da mutuwar a kalla mutane 86 bayan barkewar wani rikici mai nasaba da kabilanci a kauyukan Razat, Ruku, Nyarr, Kura da Gana-Ropp dake karamar hukumar Barkin Ladi a jihar Filato.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dubu ta cika: Kotu ta daure wata mata shekara 9 akan safarar mutane

Dubu ta cika: Kotu ta daure wata mata shekara 9 akan safarar mutane

Dubu ta cika: Kotu ta daure wata mata shekara 9 akan safarar mutane
NAIJ.com
Mailfire view pixel